An dakatar da taron da Gwamnoni su ka shirya za su yi a Abuja - NGF

An dakatar da taron da Gwamnoni su ka shirya za su yi a Abuja - NGF

Kungiyar NGF ta gwamnonin Najeriya ta bada sanarwar cewa ta fasa taron da ta shirya a makon nan. A halin yanzu an dakatar da taron sai kuma wani lokaci.

Shugaban harkokin yada labarai na kungiyar NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya bada sanarwar cewa an dage zaman da aka sa ran yi a Ranar Talata.

Alhaji Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bayyanawa Manema labarai wannan ne a Ranar Litinin, 23 ga Watan Maris, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto.

An shirya wannan zama ne domin tattauna yadda gwamnoni za su yi fama da biyan albashin ma’aikata bayan karyewar farashin danyen mai a kasuwar Duniya.

Kudin gangar mai ya yi raga-raga ne a sakamakon annobar COVID19 da ta barke. Wannan lamari dai zai shafi kasafin kudin kusan duk gwamnonin Jihohin kasar.

KU KARANTA: Coronavirus: Hadimin Shugaban kasa Kyari ya rubutawa ‘Yan Majalisa takarda

An dakatar da taron da Gwamnoni su ka shirya za su yi a Abuja - NGF
Babu ranar da kungiyar NGF za ta zauna kan batun kasafin kudi
Asali: Facebook

Kason da Gwamnoni su ke samu daga asusun gwamnatin tarayya zai ragu sosai bayan karyewar mai. A dalilin wannan ne da gwamnoni su ka shirya taro a Abuja.

A halin yanzu an dakatar da wannan taro ba tare da an bayyana dalilin yin hakan ba. Sai dai ana zargin cewa uzurin gwamnonin bai wuce na annobar Coronavirus.

Ganin Takwaransu Gwamnan jihar Bauchi ya rufe kansa a cikin daki bayan ya hadu da Mai dauke da cutar COVID-19 bai rasa nasaba da dage taron na yau.

A cikin ‘yan kwanakin nan, Bala Mohammed ya halarci taron NEC da aka yi a fadar shugaban kasa da kuma taron Gwamnonin jihohi da ya gudana a Maitama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel