Aminu Bayero ya bukaci Jama’a su dage da ruwan addu’o’i kan annobar Coronavirus

Aminu Bayero ya bukaci Jama’a su dage da ruwan addu’o’i kan annobar Coronavirus

Mun samu labari cewa Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi magana game da annobar Coronavirus wanda ta ke cigaba da girgiza Duniya.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Tuwita, Mai martaba Aminu Ado Bayero ya nuna cewa ya hau kan karagar mulkin gidan dabo a wani yanayi na damuwa.

Sarkin ya na magana ne game da cutar Coronavirus da ta shiga kasashe fiye da 100. A sakamakon barkewar COVID-19, Sarki ya bukaci jama’a su yawaita addu’o’i.

Aminu Ado Bayero ya yi kira ga Mutanen Kano su tashi tsaye da addu’o’in zaman lafiya da ganin kwanciyar hankali a daidai wannan mawuyacin hali da ake ciki.

Bugu da kari, sabon Sarkin na Kano, ya bayyanawa Talakawa cewa wannan cuta wata jarrabawa ce daga Ubangiji, don haka ya bukaci a komawa Allah da roko.

KU KARANTA: Najeriya ta bukaci a kawo mata agaji game da cutar COVID-19

Sarkin ya tunatar da jama’a cewa Allah Madaukakin Sarki mai karbar addu’ar Bayinsa ne a koda yaushe don haka su dukufa babu dare ko rana wajen neman sauki.

An daura wannan bidiyo na jawabin Mai martaba ne a dandalin sada zumunta na Tuwita a Ranar Litinin, 23 ga Watan Maris, 2020 da kimanin karfe 2:00 na rana.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kano ta dauki matakai na musamman domin ganin an gujewa barkewar wannan mummunar cuta da ke yawo watau COVID-19.

A daidai wannan lokaci kuma tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi magana daga gidansa inda ya roki a daina kawo masa ziyara har sai Coronavirus ta lafa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel