Coronavirus: Dangote ya umarci Ma’aikatansa su yi taka tsan-tsan da cuta

Coronavirus: Dangote ya umarci Ma’aikatansa su yi taka tsan-tsan da cuta

Kamfanin Dangote ya dauki mataki domin kare Ma’aikatansa da sauran jama’a daga cutar nan ta Coronavirus da ta ke yawo a kasashen Duniya daban-daban.

A wata takarda da shugaban kamfanin ya fitar a makon jiya, an bukaci ma’aikatan kamfanin su guji yin duk wani taro da zai bukaci mutum ya halarta da kansa.

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta samu labari, wannan takarda ta fito daga ofishin babban Darektan kamfanin Dangote Mista Olakunle Alake ne a Ranar Alhamis

Olakunle Alake ya bada umarnin cewa wadannan matakai za su fara aiki ne a Yau 23 ga Watan Maris, 2020. Haka zalika an hana jama’a kai wa kamfanin ziyara.

A sanarwar da aka bada, an karfafa matakai na musamman inda aka ce daga yanzu sai an cika takardun lafiya kafin a kyale Kanikawa su shiga wuraren aikin.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya hadu da Yaron Atiku mai dauke da Coronavirus

Coronavirus: Dangote ya umarci Ma’aikatansa su yi taka tsan-tsan da cuta

Ma'aikatan kamfanin Dangote za su daina karbar baki daga yanzu
Source: UGC

Alake ya bukaci ma’aikatan kamfanin su rika gudanar da duk wani taro ta kafafen sadarwa na yanar gizo kamarsu Skype, Zoom ko kuma ayi amfani da wayoyin salula.

Shugaban kamfanin na Dangote ya umarci masu juna biyu da masu fama da manyan rashin lafiya kamar larurar ciwon sukari da kuma cutar zuciya su daina zuwa ofis.

Sanarwar ta bayyana cewa duk wani wanda ya ke da matsalar numfashi da kuma ma’aikatan da su ka haura shekaru 65 za su rika yin aiki ne daga gidajensu daga yau.

Bugu-da-kari, an dakatar da duk wani horaswa da kuma taron karawa juna sani da ake yi kafin bullowar wannan cuta. Wannan doka za ta fara aiki ne na makonni biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel