Annobar Corona: Bankin Access ta garkame ofishinta a Legas bayan bullar cutar
Bankin Access ta kulle reshenta dake titin Ligali Ayorinde a cikin unguwar Victoria Island jahar Legas bayan samun guda daga cikin kwastomominta ya kamu da annobar cutar Coronavirus.
Premium Times ta ruwaito bankin ta bayyana haka ne a ranar Litinin, 23 ga watan Maris, inda ta yi kira ga duk abokan cinikiyyarta da suka shiga cikin bankin a makon da ta gabata da su killace kawunansu na tsawon kwanaki 14.
KU KARANTA: An samu karin sabbin alamomi dake bayyanar da Coronavirus a jikin dan Adam
“Mun tabbatar da wani mutumi da ya ziyarci bankinmu dake titn Ligali Ayorinde a ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2020 ya kamu da cutar Coronavirus, babu wata alama a tare da shi a lokacin da ya ziyarce mu, amma a yanzu haka yana kebance a Yaba.
“Kuma duk mutanen da suka yi mu’amala da shi wadanda aka iya samu an killace su, don haka muke kira ga duk abokan cinikiyyarta da suka shiga cikin bankin a makon da ta gabata da su killace kawunansu na tsawon kwanaki 14.” Inji ta.
Ita dai wannan mugunyar cuta ta Corona ta yi sanadiyyar mutuwar dubunnan mutane, ta karya tattalin arzikin duniya, ta yi sanadiyyar jama’a da dama sun rasa ayyukansu, ta hana tarukan jama’a, zumunci da tafiye tafiye.
A wani labarin kuma, masana kiwon lafiya a kasar Birtaniya, kwararru a sashin Kunne, Hanci da Makogwaro sun gano wasu sabbin alamomin cutar Coronavirus, daga ciki akwai daina jin dandano a harce da kuma daina gane kamshi ko wari.
Kungiyar likitocin Kunne, Hanci da Makogwaro na kasar Ingila ne suka sanar da haka, inda suka ce wadannan alamomi suna bayyana ne a inda sanannun alamomin cutar basu bayyana a jikin mai dauke da kwayar cutar ba.
Don haka suka ce duk mara lafiyan dake fama da wadannan matsaloli biyu, akwai yiwuwar yana dauke da cutar Coronavirus, saboda an samu ire iren mutanen nan a kasashen China da Kudancin Koriya, inda suka kira alamomin ‘Anosmia.’
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng