Babbar magana: Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin rufe ko ina a jihar saboda COVID-19

Babbar magana: Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin rufe ko ina a jihar saboda COVID-19

- Gwamnatin jahar Neja ta sanar da rufe harkoki a jahar, inda ya kaddamar da hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na safe zuwa 8:00 na dare

- Gwamna Sani Bello ya ce takaita zirga-zirgan zai fara ne daga ranar Laraba kamar yadda ya sanar a ranar Litinin, 23 ya watan Maris

- Ya ce akwai bukatar daukar wannan mataki sakamakon sabbin mutanen da aka samu sun kamu da cutar Coronavirus a Abuja, wanda jahar Neja ce mafi kusa da birnin tarayyar

Gwamnan jahar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sanar da rufe harkoki a jahar, inda ya kaddamar da hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na safe zuwa 8:00 na dare.

A cewar gwamnan takaita zirga-zirgan zai fara ne daga ranar Laraba kamar yadda ya sanar a ranar Litinin, 23 ya watan Maris.

Babbar magana: Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin rufe ko ina a jihar saboda COVID-19

Babbar magana: Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin rufe ko ina a jihar saboda COVID-19
Source: Twitter

Ya ce akwai bukatar daukar wannan mataki sakamakon sabbin mutanen da aka samu sun kamu da cutar Coronavirus a Abuja, wanda jahar Neja ce mafi kusa da birnin tarayyar.

A bangare guda kuma mun ji cewa Masana kiwon lafiya a kasar Birtaniya, kwararru a sashin Kunne, Hanci da Makogwaro sun gano wasu sabbin alamomin cutar Coronavirus, daga ciki akwai daina jin dandano a harce da kuma daina gane kamshi ko wari.

Kungiyar likitocin Kunne, Hanci da Makogwaro na kasar Ingila ne suka sanar da haka, inda suka ce wadannan alamomi suna bayyana ne a inda sanannun alamomin cutar basu bayyana a jikin mai dauke da kwayar cutar ba.

Don haka suka ce duk mara lafiyan dake fama da wadannan matsaloli biyu, akwai yiwuwar yana dauke da cutar Coronavirus, saboda an samu ire iren mutanen nan a kasashen China da Kudancin Koriya, inda suka kira alamomin ‘Anosmia.’

Shugaban kungiyar, Farfesa Claire Hopkins da Farfesa Nirmal Kumar ne suka fitar da sanarwar inda suka ce an fara samun ire iren almomin Anosmia a kasashen Faransa, Italy, Amurka da Birtaniya.

Don haka suka bayar da shawarar a fara amfani da wannan hanya don gane masu dauke da cutar Coronavirus amma basu tari ko atishawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel