Coronavirus: Gwamnatin Kano ta karyata labarin bullar cutar a jahar
Gwamnatin jahar Kano a ranar Litinin, 23 ga watan Maris ta bayyana cewa babu wani lamari na bullar cutar coronavirus da aka tabbatar a jahar.
Ta karyata rahotanni shafukan soshiyal midiya da kke has ashen barkewar annobar coronavirus a jahar.
A bisa ga wata sanarwa daga jami’ar labarai ta ma’aikatar lafiya, Hadiza Namadi ta ce: “An janyo hankalin ma’aikatar lafiya ta jahar Kano kan wani labarin karya da ke yawo a soshiyal misiya kan batun barkewaar cutar coronavirus a Kano.

Asali: Twitter
"An watsa labaran karyar ne a shafuka da ke dauke da lagwan CNN da BBC na bogi, kan zargin cewa wasu daliban jami’ar Bayero biyu na dauke da cutar ta coronavirus bayan yi musu gwaji.
“Tabbass labarin kanzon kurege ne, kuma ba komai bane face makircin masu son kawo tashin hankali a jahar.
“Kai tsaye, ba a taba samun lamarin barkewar cutar a jahar Kano ba tun bayan bullar cutar a kasar.
“Don haka kwamishinan lafiya a jahar,Dr. Aminu Ibrahim Tsnyawa na bukatar dukkanin kungiyoyi, da mutane da su yi watsi da labarin kamar yadda ya ke ba komai bane face karya da jita-jita da ke yawo domin haddasa fargaba a cikin jama’a.
“Sannan kwamishinan ya shawarci mutane da su dauki matakan da ya kamata kan cutar kamar wanke hannu, nisantan taron jama’a da kuma kai rahoton duk wani da ake zargi ga cibiyar lafiya mafi kusa.”
KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta yi wa dan Atiku da ya kamu da coronavirus addu’a
A bangare guda, Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, a zaben 2019 Atiku Abubakar ya sanar da cewa ɗan sa ya kamu da ƙwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus.
Atiku ya sanar da hakan ne a shafinsa na dandalin sanda zumunta na Twitter a ranar Lahadi 22 ga watan Maris na 2020.
A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya, an garzaya da dan sa zuwa asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja domin yi masa magani.
Ya kara da cewa, "An sanar da hukumar kula da Cututtuka masu saurin yaduwa ta Najeriya @NCDCGov kuma an kai shi asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a Abuja domin yi masa magani da kulawa da shi.
"Zan yi farin ciki idan za ku iya saka shi a addu'o'in ku. Ku cigaba da kiyaye wa domin Coronavirus gaskiya ne."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng