Coronavirus: Sheikh Pantami ya bayyana abin da ya sa aka tsaida karatun addini

Coronavirus: Sheikh Pantami ya bayyana abin da ya sa aka tsaida karatun addini

Mun samu labari maras dadi cewa an dakatar da karatun da aka saba yi na mako-mako a masallacin Annour da ke Unguwar Wuse II a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Annobar cutar nan ta Coronavirus ce ta sa aka dauki matakin dakatar da wannan darasi da aka saba yi duk Lahadi. A halin yanzu cutar ta addabi kasashe da dama a Duniya.

Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya bada sanarwar cewa daga yanzu za a rika bin wannan karatu ne a shafin sadarwa na Facebook kai-tsaye maimakon zuwa masallaci.

Isa Ibrahim Pantami ya yi wannan bayani ne a shafinsa na sada zumunta na Tuwita. Sanarwar ta zo ne da kimanin karfe 10:00 na daren jiya Ranar Asabar, 21 ga Watan Maris.

Haka zalika babban Malamin ya kuma bayyana cewa an tsaida karatun littafin nan Shamaa'ilun Nabiy wanda aka saba karantawa bayan sallar Magriba zuwa Ishai a masallacin.

KU KARANTA: Sarkin Daura ya jagoranci addu'o'i saboda cutar Coronavirus

A daidai wannan lokacin za a rika gudanar da wasu karatun na dabam ta kafar sada zumuntar Facebook, yayin da ake cigaba da kokarin neman kariya daga Coronavirus.

Malamin wanda yanzu ya rike da kujerar Minista a gwamnatin tarayya ya godewa Allah da aka samu kafafen sadarwa na zamani da su ke taimakawa Bayin Allah a yau.

Shehi Isa Ibrahim Pantami ya ke cewa ya zama dole a kare rayukan al’umma. A cewarsa Manzon Allah ya hana wadanda su ka ci tafarnuwa zuwa sallah saboda cutar da jama’a.

Har ila yau, babban Malamin addinin ya bayyana cewa addinin Musulunci ya nemi Bayin Allah su yi sallah a gidajensu a lokutan ruwan sama domin kare rayuka daga halaka.

A jawabin na sa, Pantami ya yi kira ayi biyayya ga Malaman kiwon lafiya wadanda su ke da ilmi a wannan harka domin kare kai daga wannan cuta da wasu ke musanyawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel