Saudiyya za ta kama wasu mutane da suka dirki maganin kashe kwayoyin cuta don tsoron kamuwa da Coronavirus

Saudiyya za ta kama wasu mutane da suka dirki maganin kashe kwayoyin cuta don tsoron kamuwa da Coronavirus

Ofishin hukunta jama’a a kasar Saudiya a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris, ya bayar da umurnin kama wasu mutane biyu da suka bayyana a wani bidiyo inda suke dirki maganin kashe kwayoyin cuta don tsoron kamuwa da Coronavirus.

An gano matasan a lokuta mabanbanta suna dirkar maganin kashe kwayoyin cutar a wani bidiyo da ya shahara, inda hakan ya haifar da zafafan sharhi a yanar gizo.

A safin Twitter, ofishin hukunta jama’ar ta yi umurnin kama mazajen kan shan sinadaren kashe kwayoyin cutar wanda bai dace da garkuwar jikin dan Adam ba da kuma batar da jama’a cewa hakan zai kare su daga cutar coronavirus.

Wani mai amfani da shafin Twitter ya nemi a yi wa mutanen biyu hukunci mai tsanani, cewa sun sanya matasa a cikin hatsari sannan kuma cewa suna iya rinjayarsu har su aikata hakan.

Saudiyya za ta kama wasu mutane da suka dirki maganin kashe kwayoyin cuta don tsoron kamuwa da Coronavirus
Saudiyya za ta kama wasu mutane da suka dirki maganin kashe kwayoyin cuta don tsoron kamuwa da Coronavirus
Asali: UGC

Kasar Saudiyya ta samu mutane 274 da ke dauke da coronavirus amma babu wanda ya mutu zuwa yanzu.

Kasar larabawar mafi girman tattalin arziki ta rufe gidajen kallo, manyan kantuna da gidajen cin abinci, da dakile jirage da kuma dakatar da Umrah a kokarinsu na hana yaduwar mummunan annobar.

KU KARANTA KUMA: An killace mutane 5 a jihar Nasarawa bayan sun nuna alamun cutar Coronavirus

Hakazalika kasar Saudiyya ta dakatar da salloli a masallatai duk a kokarinta da magance lamarin.

A wani labarin kuma mun ji cewa Masarautar Saudiyya ta hana shiga Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina, fari daga ranar Juma'a, 20 ga Maris ga masu khamsu-Salawati cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Kakakin ma'aikatar kula da lamarin Masallacin Harami da Annabi SAW dake Madina ya sanar da hakan ne ranar Juma'a.

A yanzu, mazauna cikin Masallacin da ma'aikata kadai suka sallaci sallar Asuba a yau Juma'a.

Ma'aikatar Lafiyan kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa kawo ranar Alhamis, mutane 274 sun kamu da cutar.

Sarki Salman bin Abdulaziz a jawabin da ya yiwa al'ummar kasar daren Alhamis ya bayyana cewa gwamnati da daukar dukkan matakan da ya kamata wajen yakar Coronavirus kuma ya bada tabbacin cewa za'a kaiwa ko wani dan kasa magani, abinci, da abubuwa morar rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel