Ba za mu dakatar da zama ba saboda coronavirus – Majalisar wakilai

Ba za mu dakatar da zama ba saboda coronavirus – Majalisar wakilai

- Majalisar wakilai ta ce bata tunanin dakatar da zamanta a tsaka da barkewa annobar coronavirus

- Mai magana da yawun majalisar ya ce yan majalisan za su ci gaba da zamansu domin samun damar sassaita zafafan batutuwa

- Tuni dai wasu gwamnatocin jihohi suka hana taron da ya fi na mutane 50

Majalisar wakilai ta ce bata tunanin dakatar da zamanta a tsaka da barkewa annobar coronavirus.

Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar wakilan, ya bayyana haka a yayinda ya ke jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Maris.

Akwai yan majalisa 360 a majalisar wakilan kasar da kuma dubban baki da ake samu duk mako.

Domin hana yaduwar annobar, tuni dai wasu gwamnatocin jihohi suka hana taron da ya fi na mutane 50.

Ba za mu dakatar da zama ba saboda coronavirus – Majalisar wakilai

Ba za mu dakatar da zama ba saboda coronavirus – Majalisar wakilai
Source: Facebook

Kalu ya ce yan majalisan za su ci gaba da zamansu domin samun damar sassaita zafafan batutuwa.

A ranar Laraba ne majalisa ta nemi a hana baki shiga harabar majalisar dokokin kasar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sakamakon gwaji ya nuna wanda ake zargi da coronavirus a Katsina bai da cutar

A wani labarin kuma, mun ji cewa cewa an tabbatar da samun kwayar cutar Cronavirus a jikin mutane hudu a jihar Legas.

Kwamishinan lafiya a jihar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai. Abayomi ya bayyana cewa an samu mutane hudun ne daga cikin mutane 19 da aka yi wa gwajin kwayar cutar a ranar Laraba.

Ya kara da cewa an kebe mutanen hudu da aka samu da cutar a asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba, Legas.

Ya ce daga cikin sabbin mutanen da aka samu dauke da cutar akwa wata mata da ta kamu da kwayar da cutar daga wurin mata da ta zo daga kasar Ingila kwana biyu da suka wuce.

A cewarsa, akwai kuma wata mata da ta dawo Najeriya daga kasar Faransa ranar 14 ga watan Maris a jirgin kasar Turkiyya, TK1830.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel