Yansanda sun ceto mutane 2 daga hannun yan bindiga, sun kashe gungun miyagu

Yansanda sun ceto mutane 2 daga hannun yan bindiga, sun kashe gungun miyagu

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta sanar da yi ma wasu gungun yan bindiga kisan gilla, tare da kubutar da mutane biyu da suka yi garkuwa dasu a kauyen Daku, karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

Mataimakin kwamishinan Yansandan jahar Kaduna, Onah Sunny ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis, 19 ga watan Maris, inda yace yan bindigan sun kai hari kauyen ne inda suka sace Dauda Sani da dan uwansa.

KU KARANTA: Yan Najeriya biyu, mai jego da jaririnta sun kamu da cutar Coronavirus

“Bayan an sanar da Yansanda, sai muka tura jami’an suka tare yan bindigan kafin su kai sansaninsu, a nan muka yi bata kashi dasu, muka kashe dan bindiga daya, sa’nnan muka ceto Dauda da dan uwansa.

“Sai dai dan uwan nasa yana asibiti yana samun kulawa, da yake jami’anmu sun nuna ma yan bindigan fin karfi, ala dole suka tsere, suka jefar da baburansu guda shida. Haka zalika mun kwace bindigu 2 kirar AK-47, alburusai, wayoyin salula kirar Techno, fitila, layu da kudi N268,000.” Inji shi.

Mista Onah ya yi kira ga jama’a su cigaba da sanar da Yansanda rahoton duk wasu bata gari a kan lokaci domin su samu daman basu kariya da dukiyoyinsu. Haka zalika ya nanata manufar rundunar na tsaftace Kaduna daga kowanne irin miyagun ayyuka.

A wani labari kuma, ministan kula da al’amuran Yansandan Najeriya, Muhammad Dingyadi ya bayyana cewa nan bada jimawa ba hukumar Yansanda za ta fara daukan sabbin kuratan Yansanda 10,000 a duk fadin Najeriya.

Hakan na daga cikin cika alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na samar da sabbin jami’an Yansanda 40,000 a tsawon shekaru hudu na wa’adin mulkinsa.

Dingyadi ya bayyana cewa sun fara tsara yadda daukan aikin zai kasance, wanda suke sa ran zai kara adadin jami’an Yansandan Najeriya tare da taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel