Gwamna Dapo Abiodun ya hana gidan rawa da kallon fim aiki a Ogun

Gwamna Dapo Abiodun ya hana gidan rawa da kallon fim aiki a Ogun

A Ranar Laraba, 18 ga Watan Maris, 2020, gwamnatin jihar Ogun, ta haramta manyan taron da za su iya jawo cunkuso na mutane akalla 50 ko kuma fiye da haka.

Wannan ya na cikin kokarin da gwamnatin ta ke yi na hana yaduwar cutar coronavirus a jihar Ogun. Daga cikin wuraren da aka hana budewa akwai gidajen rawa.

Gwamnati ta bada umarnin rufe dakunan taro, da gidajen kallo da casu. Haka zalika za a rufe duk wuraren cin abinci da tashoshi hawa yanar gizo da wuraren wasanni.

Babban Sakataren yada labaran gwamnatin jihar Ogun, Kunle Somorin, ya bada wannan sanarwa. Sakataren gwamnan ya ce wannan doka za ta fara aiki na wata guda.

A cewar Kunle Somorin, ba a tauye hakkin jama’a wajen daukar wannan mataki ba. Gwamnatin Dapo Abiodun ta ce zaman lafiya mutanenta shi ne gaba da komai.

KU KARANTA: Direba ‘Dan shekara 38 da ya kamu da cutar Coronavirus a Ekiti

Gwamna Dapo Abiodun ya hana gidan rawa da kallon fim aiki a Ogun
Dapo Abiodun ya ce a rufe inda jama'a za su rika taruwa
Asali: Twitter

Har ila yau, Mai girma gwamnan na Ogun ta bakin Kunle Somorin, ya bayyana cewa zai cigaba da ganawa da Masu ruwa da tsaki a jihar domin maganin wannan annoba.

Gwamnan ya bayyana cewa zai zauna da shugabannin addini da masu makarantu domin jin ta bakinsu. Babu mamaki a kara wa’adin wannan doka ko kuma a rage.

“Bayan matakan da aka dauka a halin yanzu a yunkurin takaita yaduwar cutar coronavirus, gwamnati ta ga matukar bukatar sanar da wadannan sababbin matakai:”

“Haramta duk wani dandazon da zai jawo haduwar mutane 50 ko fiye a wuri guda kamar wurin rawa da casu, dakin taro, dakunan taro, wuraren cin abinci, da wasanni.”

Jawabin ya nuna cewa wannan mataki zai fara aiki ne ba tare da wata-wata ba. Ana kuma sa ran a karon farko a shafe wata guda ana dabbaka wannan hani a jihar Ogun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng