An sake samun sababbin masu dauke da cutar Coronavirus a kasar Saudi

An sake samun sababbin masu dauke da cutar Coronavirus a kasar Saudi

Rahotanni daga jaridar Saudi Gazette sun kawo rahoton cewa Kasar Saudi Arabia ta tabbatar karawar samun wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus a farkon makon nan.

A Ranar Laraba, 18 ga Watan Maris, kasar Saudi ta bayyana cewa mutane 67 sun kamu da wannan cuta. Wannan ya sa adadin masu dauke da cutar ta Coronavirus su ka karu.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Saudi ta ce daga cikin mutane 67 da su ka kamu da cutar kwanan nan, akwai muane 45 wadanda su ka ziyarci kasashen ketare a ‘yan kwanakin nan.

Jawabin da aka fitar ya bayyana cewa wadannan Bayin Allah sun samo cutar ne daga kasashen Ingila, Turkiyya, Sifen, Switzerland, Faransa, Indonesiya da kuma kasar Iraki.

Kawo yanzu an killace wadanda su ka kamu da wannan cuta. Akwai mutane 19 da ke dauke da cutar a Riyadh. 13 su na Jidda, Mutane 11 kuma su na jinya ne a Birnin Makkah.

KU KARANTA: Mane ya ba Kasar Sanagal tkyautar kudi domin yakin Coronavirus

An sake samun sababbin masu dauke da cutar Coronavirus a kasar Saudi
Masu dauke da cutar Coronavirus a kasar Saudi sun kai 230
Asali: UGC

Har ila yau akwai mutane 23 da ake da labarin sun kamu da wannan cuta a Gabashin kasar. Amma akwai mutane shida da su ka warke a halin yanzu bayan an tirke su a asibiti.

Rahoton ya bayyana cewa yanzu akwai akalla mutane 238 da su ke dauke da cutar Coronavirus a kasar Larabawan. A dalilin haka ne gwamnati ta dauki wasu tsauraran matakai.

Labarin da mu ke samu shi ne Majalisar malaman Saudi ta dakatar da yin sallar jam’i har da kuma sallar Juma’a a cikin masallatan da ke cikin kasar domin rage yaduwar cutar.

Wannan doka ba za ta yi aiki ba ne kawai a masallatan harami na Biranen Makka da Madina kamar yadda hukumomin gwamnati su ka bayyana a Ranar Talatar da ta gabata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel