Dalilin da yasa aka rage farashin litar man fetur - Oshiomhole
Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan amincewa da yayi na rage farashin man fetur daga N145 zuwa N125.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da babban sakataren yada labaransa, Simon Ebegbulem ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Ya kwatanta hukuncin shugaban kasar da "amfanin shugabanci na gari da kuma gwamnati mai jin kai da kukan jama'a."
Kamar yadda takardar ta kunsa: "A madadin kwamitin ayyuka na wanna jam'iyyar mai daraja ta APC, ina jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan hukuncin amincewa da rage farashin kudin man fetur daga N145 zuwa N125.
"Wannan ya nuna yadda gwamnatin APC ta mayar da hankali wajen daidaita rayuwar jama'a. Hakan kuwa zai sa sunan gwamnatin Buhari ya hau rubutun dutse ta yadda aka sauke farashin man."
Oshiomhole ya bayyana cewa rage farashin ya nuna cewa shugaba Buhari mutum ne mai ra'ayin cigaban kasa da jama'arta.
DUBA WANNAN: Zargin badakala: Kotu ta tsayar da ranar fara sauraron korafin tsohon sarki Sanusi II
Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatin APC a karkashin jagorancin shugaba Buhari ta tabbatar wa da duniya cewa tana jin tausayin jama'arta tare da kokarin ganin ta saukaka musu rayuwa ta kowanne fanni a yayin da tattalin arzikin duniya ke yin kasa sakamakon annobar bullar kwayar cutar 'Coronavirus'.
A ranar Laraba ne Legit.ng ta rawaito cewa alamu na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da rage farashin litar man fetur zuwa N125 daga tsohon farashinsa, N145.
A cewar Legit.ng, majiyarta a fadar shugaban kasa ta sanar da ita cewa shugaba Buhari zai amince da bukatar rage kudin farashin litar man bayan karamin ministan man fetur na kasa, Timipre Sylva, ya gabatar da bukatar neman yin hakan yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da ake yi duk sati a fadar shugaban kasa.
A cewar majiyar, wacce bata amince a ambaci sunanta ba, Sylva ya gabatar da bukatar rage farashin litar man fetur din ne biyo bayan zabgewar farashin danyen man fetut a kasuwar duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng