Na yafewa wadanda su ka nemi su tunbukeni daga kujera - Oshiomhole

Na yafewa wadanda su ka nemi su tunbukeni daga kujera - Oshiomhole

A kokarin kawo karshen rikicin da ya dabaibaye APC, shugaban jam’iyyar na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ce ya yafewa duk wadanda su ka saba masa.

Legit.ng za ta tuna cewa an kai daf da tunbuke Adams Oshiomhole daga shugaban APC. Kotun daukaka kara ce ta ceci jagoran jam’iyyar daga dakatarwar da aka yi masa.

Da ya ke magana da ‘Yan jarida a Hedikwatar jam’iyya Ranar Talata, 17 ga Watan Maris a Abuja, Oshiomhole ya bayyana cewa ya manta da tuggun da aka rika kitsa masa.

Oshiomhole ya yi wannan jawabi ne bayan ya jagoranci taron NWC daga dawowarsa aiki. “Abin da ya hadamu ya fi karfin kananan sabaninmu da su ka jawo mana rigima.”

“A bangarena, na fadawa kowa ya amince da abin da su ke tunanin rauni ne daga wuri na. Na roki su yafe mani, kuma sun yafe mani.” A cewar shugaba Adams Oshiomhole.

KU KARANTA: Osita Okechukwu ya fadawa Tinubu matsalolin Oshiomhole

Na yafewa wadanda su ka nemi su tunbukeni daga kujera - Oshiomhole
Oshiomhole ya bukaci a manta da abin da ya faru a APC
Asali: UGC

Shugaban jam’iyyar ya ce marada sun ji kunya yanzu: “Ina mai tabbacin cewa ‘Yan adawa za su yi bakin ciki na san har wadansu sun fara shirin ganin rigima ta barke mana.”

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya kuma fadawa Manema labaran cewa: “Na yafewa wadanda su ka fusata ni, kamar yadda ni ma wadanda na batawa rai, su ka yafe mani.”

A cewarsa, dadin abin shi ne, wadanda ransu ya baci a tafiyar jam’iyyar sun hakura da abin da ya faru, sun kuma ajiye banbancinsu a gefe, domin ganin cigaban jam’iyyar APC.

“Na yi afuwa ga duk wani abin bacin rai da na ke samu daga rauni na wani, haka ya kamata. Zai zama ba daidai ba ne kawai idan mun iya fada, amma ba mu iya sulhu ba.” Inji sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel