Shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kaduna ya mutu
Allah ya yi wa Malam Sani Dalhatu Musa, shugaban hukumar jin dadin alhazan jihar Kaduna, rasuwa a yau, Laraba.
Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa shugaban hukumar ya mutu ne sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Malam Sani ya zama shugaban hukumar ne a watan Janairu 2020 bayan ya shafe fiye da shekaru 20 yana aiki tare da hukumar ta jin dadin alhazan jihar Kaduna.
Ya taba rike shugabancin hukumar a karamar Birnin Gwari, Igabi da sauran wasu kananan hukumomin jihar Kaduna.
Kazalika, ya taba rike mukamin shugaban aiyuka na aiyuka a hukumar kafin daga bisani ya zama shugaban aiyuka na hukumar a jihar Kaduna.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng