Likitoci sun tafi yajin aikin sai baba ya gani a Gombe duk da barkewar coronavirus

Likitoci sun tafi yajin aikin sai baba ya gani a Gombe duk da barkewar coronavirus

Duk da barkewar annobar cutar coronavirus a Najeriya, likitoci da ke aiki tare da gwamnatin jahar Gombe sun tafi yajin aiki na sai baba-ya-gani.

Hakan ya biyo bayan rashin tsayar da magana guda a tsakanin kungiyar likitocin da gwamnatin jahar bayan tattaunawa daban-daban da suka yi.

Kungiyar likitoci a Gombe sun ce sun gaji da rashin cika alkawarin gwamnatin.

Likitoci sun tafi yajin aikin sai baba ya gani a Gombe duk da barkewar coronavirus
Likitoci sun tafi yajin aikin sai baba ya gani a Gombe duk da barkewar coronavirus
Asali: UGC

Shugaban kungiyar, Dr Saidu Alhassan a wani taron manema labarai a Gombe ya ce likitocin sun tafi yajin aiki bayan rashin samun matsaya da gwamnatin jahar tsawon makonni 11.

Ya bayyana cewa sauran likitocin da ke nan, aiki ya karu masu sosai yayin da har yanzu aka gaza inganta jin dadinsu.

Kungiyar ta ce lallai ba komai take so ba face kare hukumar lafiyar.

Tawagar gwamnatin ta ce tana da karfin gwiwar cewa za a shawo kan komai bad a jimawa ba.

Matsalar a yanzu shine yadda matakin kungiyar zai shafi al’umma.

Gwamnatin na aiki don rage tasirinta kan hukumar lafiya a cikin jahar.

Daga gwamnati har likitocin da ke yajin aiki na so a saurari sakonninsu da kuma kokarin sanya tausayin kansu a zukatan jama’a.

KU KARANTA KUMA: Annobar Corona: Hukumar NYSC ta kulle sansanonin horas da yan bautan kasa

A halin da ake ciki, kwamishinan lafiya Dr. Ahmad Gana ya yi Allah wadai da matakin tafiyar yajin aikin cewa hakan ya saba ma koyarwar likita, da kuma nuna rashin kulawar kungiyar ga halin da jama’a ke ciki.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage bikin wasanni na kasa (NSF) da aka yi wa lakabi da Edo 2020 a matsayin wani mataki na kare yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

Ministan Wasanni na Najeriya Sunday Dare ya sanar da cewa za a dage wasanni na kasar da aka shirya yi a Birnin Benin na jihar Edo.

'Yan wasa a dukkan jihohin kasar sun dade suna shirin zuwa Birnin Benin domin hallartar wannan wasannin kafin sanarwar ta fito a ranar Talata 17 ga watan Maris.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel