An tashi babu matsaya a taron Gwamnatin Tarayya da Malaman Jami’a

An tashi babu matsaya a taron Gwamnatin Tarayya da Malaman Jami’a

Muhimmin zaman da aka yi tsakanin kungiyar ASUU ta Malaman jami’o’i da gwamnatin tarayya bai iya kawo karshen yajin aikin da ake fama da shi a yanzu.

Rahotanni sun zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa ba a samu wani daidaito a taron da aka yi Ranar Talata tsakanin gwamnati da kungiyar Malaman jami’o’i ba.

Kamar yadda mu ka samu labari dazu an dauki akalla sa’a takwas gwamnatin Najeriya ta na ganawa da shugaban kungiyar ASUU ta Malamai da ke ta yajin aiki.

Jaridar ta ce ba a yi iya samun matsaya game da batutuwan da aka tattauna a kai ba. Wannan ya sa a karshen taron ba a cin ma yarjejeniyar janye yajin aikin da ake yi ba.

A farkon makon jiya ne kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aikin mako biyu a sakamakon sabawa wasu yarjejeniya da gwamnati ta yi, da kuma hana Malamai albashi.

KU KARANTA: Kungiyar SSANU ta ce ba ta ji dadin shiga tsarin IPPIS ba

An tashi babu matsaya a taron Gwamnatin Tarayya da Malaman Jami’a
Ministocin kwadago, ilmi da Shugaban NUC sun zauna da ASUU
Asali: Depositphotos

A watan Fubrairu da ya gabata, gwamnatin tarayya ta ki biyan Malaman makarantun jami’o’in da ba su shiga cikin tsarin albashin IPPIS, hakan ya sa aka rufe jami’o’i.

An yi wannan taro na jiya ne a babban ofishin Ministan kwadago da ayyukan yi na Najeriya, Dr. Chris Ngige, a Abuja. An raba zaman da aka yi ne zuwa kashi biyu.

A kashin farko na zaman, kungiyar ASUU da gwamnati sun yi magana game da halin da ake ciki. Daga baya kuma aka koma kan diddikin abubuwan da su ka jawo yajin.

Idan ba ku manta ba a makon da ya gabata ne ASUU ta fara zama da Ministocin Najeriya, a wannan zama ne aka fara shawarar jefa Malaman cikin tsarin albashin UTAS.

Biodun Ogunyemi ya ce za su sanar da ‘Ya ‘yan ASUU tayin da gwamnati ta yi masu kafin su dauki mataki. Ministoci uku da wasu manyan gwamnati sun halarci taron.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel