Ronaldo ya mayar da otel din shi na CR7 zuwa asibiti domin a dinga kula da masu Coronavirus
Bayan yaje kasar Portugal domin duba mahaifiyarsa, Maria Dolores Aveiro, wacce ta dauki tsawon lokaci babu lafiya, dan wasan mai shekaru 35 ya cigaba da zama a kasarsa ta haihuwa domin kebance kanshi daga sabuwar cutar Coronavirus mai kisa
Ya yanke wannan shawara ne bayan an tabbatar da cutar a jikin daya daga cikin dan kungiyarsu ta kwallon kafa ta Daniele Rugani, wanda kuma aka yi msa hoto da sauran abokanansa kwana daya kafin ayi masa gwajin.
Abin jin dadin dai shine, babu wata shaida dake nuna cewa dan wasan da sauran danginsa suna dauke da wannan cuta, hakan ya sanya dan wasan amfani da damar da yake da ita wajen yaki da wannan cutar.
Ronaldo ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda ya ce: "Duniya na cikin babban tashin hankali, inda hakan yake bukatar mu mayar da hankulan mu.
"Ina magana daku a yau ba a matsayin dan wasa ba, ina magana daku ne a matsayin danku, kuma uba, sannan kuma dan adam wanda yake cikin damuwa akan abinda yake faruwa a duniya.
"Yana da matukar muhimmanci muyi amfani da shawarar da hukumar lafiya ta duniya ta bamu, da sauran hukumomi masu fada aji akan yadda zamu kula da kanmu akan wannan lamarin. Kula da lafiyar al'umma ne abu mafi muhimmanci a wannan lokacin.
"Ina so na aika da sakon ta'aziyyata ga duk wanda ya rasa wani nasa sanadiyyar wannan lamarin, sannan kuma ina jinjina ga wadanda suke yin kokari wajen kawo karshen wannan cuta."
A cewar Marca, dan wasan ya bayyana kudurinsa na mayar da daya daga cikin otel dinsa dake kasar Portugal ya mayar dashi wajen da za a dinga lura da masu cutar ta Corona.
Dakunan za a dinga amfani dasu ba tare da an biya ko sisi ba, sannan kuma Ronaldo da kanshi zai dinga biyan likitoci da kudin magani.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng