Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da Diri a fadar Shugaban kasa (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 17 ga watan Maris, ya gana da sabon gwamnan jahar Bayelsa, Sanata Douye Diri, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wannan shine karo na farko da shugabannin biyu ke shiga labule a ofishin Shugaban kasar.
Bayan nan Diri ya fada ma manema labarai cewa shugaba Buhari ya ji dadin yadda ya ke tafiyar da lamura tun bayan da ya hau kujerar shugabanci a ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
Ga hotunan ganawar tasu a kasa:
Kotun koli ce ta mika wa Diri wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) nasara biyo bayan badakalar takardar karatu na abokin takarar dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Biobarakum Degi-Eremienyo.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya koma bakin aiki
A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Adams Oshiomhole, ya kai ziyara zuwa fadar shugaban kasa a Ranar Litinin.
Kamar yadda mu ka samu labari, Kwamred Adams Oshiomhole ya samu ganawa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa watau Alhaji Abba Kyari a ziyarar da ya kai.
Sai dai Oshiomhole bai iya haduwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, wanda a lokacin ana tunanin ya na tare da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamilla.
Bayan ya gana da Rt. Hon. Femi Gbajabiamilla, shugaban kasar ya halarci bikin Expo 2020 wanda ma’aikatar kimiyya da fasaha ta shirya a filin Eagles Square da ke Garin Abuja.
Wata majiya daga cikin fadar shugaban kasar ta ce Adams Oshiomhole ya shiga ofishin Abba Kyari ne da rana. ‘Yan jarida ba su iya samun labarin wannan tattaunawa ba.
Ko da shugaban na APC na kasa bai yi wa Manema labarai magana game da wannan zama ba, Legit.ng Hausa ta fahimci cewa zaman bai rasa nasaba da rikicin cikin gida.
Oshiomhole ya ziyarci fadar shugaban kasar ne jim kadan bayan kotun daukaka kara ta yanke hukunci, ta ba shi nasara bayan an dakatar dashi daga kujerarsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng