Yanzu Yanzu: Oshiomhole ya koma bakin aiki
- Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole ya isa sakatariyar jam’iyyar domin komawa bakin aiki
- Hakan na zuwa ne bayan an kullesakatariyar tsawon wasu makonni biyu bayan dakatar dashi da wata kotu ta yi
- A yanzu haka zai jagoranci wa ganawa da jiga-jigan jam'iyyar
Shugaban Jam’iyyar All Progressive Congress na kasa, Adams Oshiomhole ya isa sakatariyar jam’iyyar domin komawa bakin aiki.
An bude ofishin Shugaban jam’iyyar wanda aka rufe tsawon wasu makonni domin ya koma bakin ayyukansa.
Ana shirin gudanar da wata ganawa na kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda Oshiomhole zai jagoranta inda wannan ne zai zamo aiki na farko da zai gabatar bayan umurnin kotun da ta sallame shi.
Mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa daga yankin arewa maso gabas, Mustapha Salihu ma ya kasance a sakatariyar.
A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwmanonin Jihohin APC sun zabi su dakatar da taron NEC da a baya aka shirya cewa za ayi a Ranar Talata, 17 ga Watan Maris.
Shugabannin APC sun dakatar da wannan taro na majalisar zartarwa zuwa wani lokaci. Shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu ya bayyana wannan Ranar Litinin.
Daily Trust ta ce Gwamnan jihar Kebbin ya dakatar da wannan zama na NEC ne domin hana jam’iyyar wargajewa a sakamakon rikicin gidan da ake fama da shi a yanzu.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatar da bikin wasanni na Najeriya na 2020 saboda Coronavirus
Wata majiya daban ta bayyana cewa har yanzu wadanda ba su tare da Adams Oshiomhole sun koma gefe guda su na tsara yadda za a tsige shugaban jam’iyyar a wannan zama.
Kafin sa bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari a farkon makon nan, Jaridar ta bayyana cewa ana ganin za a yi amfani da majalisar NEC wajen tunbuke Adams Oshiomhole.
Gwamnan jihar Edo watau Godwin Obaseki da wasu gwamnonin APC wanda ba su da rinjaye ne su ke kutun-kutun na ganin an yi waje da Oshiomhole daga kujerarsa.
Babban Jigon APC a Kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, da Magoya bayansa su na cikin wadanda ke marawa shugaban jam’iyyar ta APC na kasa baya a yanzu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng