Corononavirus: Majalisa ta bukaci Buhari ya hana baki shigowa

Corononavirus: Majalisa ta bukaci Buhari ya hana baki shigowa

Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar haramta wa baki daga kasashen da ke da yawan wadanda suka cutar coronavirus shigowa kasar.

Majalisar ta gabatar da wannan bukata ne bayan wani jawabin jan hankali da Ibrahim Oloriegbe, Shugaban kwamitin majalisar kan lafiya ya yi.

Najeriya ta samu mutum na uku da ke dauke da cutar coronavirus a ranar Talata wadanda aka alakanta da kasashen Italy da Birtaniya, wadanda suna daga cikin kasashen da ake da yawan wadanda suka kamu.

Kafin sanar da sake samun mutum na uku da ke sauke da cutar, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta hana baki shigowa kasar saboda cutar coronavirus ba.

Corononavirus: Majalisa ta bukaci Buhari ya hana baki shigowa

Corononavirus: Majalisa ta bukaci Buhari ya hana baki shigowa
Source: UGC

Sai dai Oloriegbe, ya ce baya ga hana baki shigowa, ya kamata yan Najeriya ma su guji zuwa kasashen da ke da yawan mutanen da suka kamu domin gudin yada cutar.

Har ila yau ya kuma bukaci gwamnati da ta kara kaimi wajen duba masu shigowa a filayen jiragen sama.

Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya aminta da bukatarsa, sannan ya kara da cewa a mayar da hankali sosai ga cibiyoyin killace wadanda ake zargin sun kamu da kuma na gwaje-gwaje.

KU KARANTA KUMA: Babu bukatar hana baki shigowa Najeriya saboda coronavirus – Gwamnatin tarayya

A halin da ake ciki, mun ji a baya cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage bikin wasanni na kasa (NSF) da aka yi wa lakabi da Edo 2020 a matsayin wani mataki na kare yaduwar cutar Coronavirus a kasar.

Ministan Wasanni na Najeriya Sunday Dare ya sanar da cewa za a dage wasanni na kasar da aka shirya yi a Birnin Benin na jihar Edo.

'Yan wasa a dukkan jihohin kasar sun dade suna shirin zuwa Birnin Benin domin hallartar wannan wasannin kafin sanarwar ta fito a ranar Talata 17 ga watan Maris.

Najeriya ta tabbtar da samun bullar cutar ta COVID-19 karo na uku a ranar Talata 17 ga watan Maris na 2020.

An tabbatar da kwayar cutar ne a jikin mace 'yar Najeriya da ta dawo kasar daga Birtaniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel