Babu bukatar hana baki shigowa Najeriya saboda coronavirus – Gwamnatin tarayya

Babu bukatar hana baki shigowa Najeriya saboda coronavirus – Gwamnatin tarayya

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin tarayya ta ce ta aminta da irin matakan da ta dauka don hana yaduwar annobar cutar coronavirus a Najeriya.

Najeriya na cikin kasashen Afirka 26 da cutar coronavirus ta bulla, kuma wasu kasashen sun dauki matakai na haramta taron jama'a da rufe iyakoki da dakatar da zirga-zirga daga kasashen da cutar ta fi shafa domin dakile bazuwarta a kasashensu.

A yanzu haka mutum uku aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a kasar, kuma gwamnatin kasar ta ce zuwa yanzu ba za ta haramta zirga-zirga kan wata kasa ko sufurin jiragen sama ba saboda tsoron bazuwar coronavirus.

Babu bukatar hana baki shigowa Najeriya saboda coronavirus – Gwamnatin tarayya

Babu bukatar hana baki shigowa Najeriya saboda coronavirus – Gwamnatin tarayya
Source: UGC

Ma'aikatar lafiya a kasar ta ce sun dai dauki karin matakai don kare bazuwar cutar, tare da karfafa hanyoyin bin sawun mutanen da suka yi hulda da masu dauke da cutar.

Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatin tarayya ta gamsu da irin matakan da aka dauka don hana yaduwar cutar a kasar.

Ya ce ana gwaji a filayen jiragen sama da ake shigowa daga kasashen waje, kuma a yanzu gwamnati ba ta bukatar daukar matakan hana zirga-zirgar jiragen da ke fitowa daga kasashen da cutar ta fi shafa.

KU KARANTA KUMA: Rusau: Jama'ar jihar Kaduna sun yi wa El-Rufai ihun 'Bama yi', 'Bama so' (Bidiyo)

Ya kuma ce akwai kwamiti da gwamnati ta kafa gwamnani karkashin jagorancin sakataren gwamnati domin bunkasa matakan da ake dauka.

Ya ce babu ribar zuzuta abu, domin daukar wasu matakai na iya rikita al'ummar kasa game da cutar.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Gwamnatin jahar Lagas ta tabbatar da samun mutum na uku da ke dauke da cutar Coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar, Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata, 17 ga watan Maris.

Mutum na ukun ta kasance mace mai shekara 30. Ta kuma dawo ne daga Birtaniya a ranar 13 ga watan Maris, inda bayan isowarta sai ta killace kanta, sannan ta dinga ganin alamun cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel