Yanzu Yanzu: Kotun koli ta jingine bukatar APC na sake duba hukuncinta a kan zaben Zamfara

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta jingine bukatar APC na sake duba hukuncinta a kan zaben Zamfara

Kotun koli ta dage zama kan hukuncinta game da wani kara da bangaren Abdulaziz Yari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka shigar kan sake duba hukuncinta na ranar 24 ga watan Mayu 2019 kan rikicin cikin gida na APC a Zamfara. A yanzu haka ba a tsayar da rana don zama kan lamarin ba.

Kotun daukaka karar, a hukuncinta, ta yanke cewa APC bata gudanar da zabukan fidda gwani na hakika ba a zaben 2019, sai ta soke nasarar jam’iyyar a zaben sannan ta yi umurnin ba jam’iyyar da ta zo ta biyu a zaben nasarar.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jahar Zamfara ce ta amfana daga umurnin kotun.

Amma, a wani kara da lauyan bangaren Yari na APC a Zamfara, Robert Clarke (SAN) ya fafata a ranar Talata ya roki kotun da ta sake duba umurnin, kan hujjojin cewa anyi kuskure wajen yanke ta.

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta jingine bukatar APC na sake duba hukuncinta a kan zaben Zamfara

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta jingine bukatar APC na sake duba hukuncinta a kan zaben Zamfara
Source: UGC

Clarke ya yi korafin cewa kamata ya yi kotun koli ta umurci APC da INEC da su sake gudanar da sabon zaben fidda gwani da kuma zabe a jahar Zamfara maimakon soke nasarar jam’iyyar.

Ya yi korafin cewa umurnin kotun kolin ya ba PDP, wacce bata kasance jam’iyya a cikin rikicin cikin gida na APC ba a Zamfara damar amfana daga sakamakon rikicin.

A nashi bangaren, lauyan bangaren sanata Kabir Marafa, na APC a Zamfara, Mike Ozokhome (SAN) ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar tare da tara mai yawa.

Ozekhome ya yi korafin cewa, ba wai cewar karar bai da faída na kawai, a’a ya ci zarafin tsarin kotun.

Ya kara da cewa, duba ga hukunce-hukuncen da kotun kolin ta yanke kan rikicin zabukan gwamna a jihohin Imo da Bayelsa, kamata ya yi ace masu karar sun janye cikin lallami.

Ozekhome ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar tare da tara.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: An sake samun mutum na 3 da ke dauke da Coronavirus a jahar Lagas

Bayan sauraron lauyoyin, Shugaban alkalan Najeriya, Justis Ibrahim Muhammad wanda ya jagoranci kwamitin mutum biyar da suka saurari karar, ya sanar da cewar an jingine hukuncin kotun har sai an sanar da bangarorin ranar zama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel