Yanzun-nan: An sake samun mutum na 3 da ke dauke da Coronavirus a jahar Lagas

Yanzun-nan: An sake samun mutum na 3 da ke dauke da Coronavirus a jahar Lagas

- An sake samun mutum na 3 da ke dauke da Coronavirus a jahar Lagas

- A wannan karon wata mace mai shekara 30 da ta dawo daga kasar Birtaniya ce aka samu dauke da cutar

- An yi mata gwaji aka kuma tabbatar ta kamu da Covid-19, inda a halin yanzu take wata cibiyar lafiya a Legas

- Gwamnatin jahar Lagas ce ta tabbatar da lamarin a yau Talata, 17 ga watan Maris

Gwamnatin jahar Lagas ta tabbatar da samun mutum na uku da ke dauke da cutar Coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar, Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata, 17 ga watan Maris.

Mutum na ukun ta kasance mace mai shekara 30. Ta kuma dawo ne daga Birtaniya a ranar 13 ga watan Maris, inda bayan isowarta sai ta killace kanta, sannan ta dinga ganin alamun cutar.

Yanzun-nan: An sake samun mutum na 3 da ke dauke da Coronavirus a jahar Lagas
Yanzun-nan: An sake samun mutum na 3 da ke dauke da Coronavirus a jahar Lagas
Asali: Twitter

An yi mata gwaji aka kuma tabbatar ta kamu da Covid-19, inda a halin yanzu take wata cibiyar lafiya a Legas.

Wannan lamari na zuwa ne yan kwanaki bayan gwamnatin jahar ta tabbatar da cewar mutum na biyu da ke dauke da cutar ya warke.

KU KARANTA KUMA: Yadda Mama Boko Haram da wasu suka karkatar da kudin kwangila N111.7m - Shaida

A wani labarin kuma, mun ji cewa Wata kungiyar mabiya addinin Hindu da ke kasar Indiya sun hada liyafar shan fitsarin Shanu don garkuwa daga cutar Coronavirus.

Mutane da yawa daga cikin mabiya addinin Hindu din na bautar Shanu ne kuma suna shan fitsarin shi da niyyar ya kare su daga cutuka masu tarin yawa.

Kwararru sun bayyana cewa fitsarin shanun baya maganin kowacce cuta har da cutar daji, kuma babu wata alama da ke bayyana yana maganin cutar Coronavirus din.

Liyafar, wacce kungiyar mai suna Akhil Bharat Hindu Mahasabha ta dauka nauyi anyi a hedkwatartsa da ke babban birnin kasar, ta samu halartar mutane 200. Hakazalika wadanda suka shirya liyafar na fatan shirya irinta a cikin India.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel