Yanzu nan: Shugabannin Jam’iyyar APC za su zauna taron NWC - Issa-Onilu

Yanzu nan: Shugabannin Jam’iyyar APC za su zauna taron NWC - Issa-Onilu

A karshe bayan doguwar ja-in-ja tsakanin bangarorin jam’iyyar APC mai mulki, mun samu labari cewa an sa ranar da za ayi taron NEC na majalisar gudanarwa ta NWC.

Legit.ng ta samu labari dazu cewa jam’iyyar APC ta shirya wannan zabe ne a Ranar Talata 17 ga Watan Maris 2020. Za a yi zama ne a babbar Sakatariyar jam’iyyar APC.

Jam’iyyar ta na gayyatar duk wani da ke cikin majalisar NWC mai alhakin aikaca-aikacen APC na yau da kullum ya halarci wannan taro da za ayi a babban birnin tarayya.

Daga cikin abubuwan da za a tattauna a taron goben akwai batun kujerar shugaban APC, Kwamred Adams Oshiomhole, wanda kotu ta dakatar daga matsayin da ya ke kai.

Idan ba ku manta ba, kwanaki wani Alkalin babban kotun tarayya ya bada umarnin cewa Oshiomhole ya daina yawo da sunan shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa.

KU KARANTA: APC: Oshiomhole ya samu nasara a kotun daukaka kara

A Ranar Litinin dinnan, 16 ga Watan Maris, 2020, babban kotun daukaka kara ta zauna inda ta fara yanke hukunci game da wa’adin Oshiomhole a kujerar jam’iyyar APC.

Kamar yadda bayanin da aka fitar a yau Ranar Litinin ya nuna, za a soma wannan taro ne da karfe 12:00. Ana sa ran cewa za a kakkabe duk matsalolin da ke damun jam’iyyar.

Wannan sako ya fito ne daga bakin babban Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Mallam Lanre Issa-Onilu, a madadin daukacin majalisar NWC na jam’iyyar.

Yanzu haka dai ana ta samun rikicin cikin gida a jam’iyyar APC inda har kotu ta ba mataimakin Sakatare na kasa, Victor Gaidom damar darewa kan kujerar Adams Oshiomhole.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel