Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu

Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu

Wata babbar kotun tarayya a Abuja a ranar Litinin, 16 ga watan Maris, ta umurci Shugaban hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai da ya mika sojojin da ake zargi da hannu wajen sakin Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume bayan jami’an yan snada sun kama shi.

Justis Binta Nyako ta umurci Shugaban rundunar sojin ko kuma duk wani da ke rike da masu laifin da su mika su a kotu a ranar 30 ga watan Maris.

A watan Agustan da ya wuce 'yan sanda suka kama shi a jihar Taraba da ke arewacin kasar bayan da suka yi zarginsa da hannu wajen satar mutane domin karbar kudin fansa.

Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu

Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu
Source: UGC

Sai dai a wancan lokacin rundunar 'yan sandan ta zargi wasu sojojin kasar da hallaka jami'anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wuta kan tawagar 'yan sandan da ta kamo Wadume.

Lauya mai gabatar da kara, Simon Lough ne ya bukaci kotun da ta tilasta wa manyan jami'an sojin da su yi hakan domin wadanda ake zargin su fiuskanci shari'a.

Kotun dai ba ta saurari ta bakin Hamisu Bala Wadume da sauran wadanda ake tuhuma ba, kasancewar sojojin da ake zargin ba su bayyana a kotun ba.

A ranar 6 ga watan Agustan bara ne wani ayarin rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da masu satar mutane da 'yan fashi ta yi artabu da wasu sojoji a jihar Taraba da arewa maso gabashi Najeriya.

Hakan ya faru ne lokacin da 'yan sandan, dauke da hamisu Wadume cikin sarka suka ta samma wani shinge da sojojin suka kafa, inda sojojin suka bude musu wata, har wasu daga cikin 'yan sandan suka riga mu gidan gaskiya.

KU KARANTA KUMA: Cutar Coronavirus ba ta shigo Yobe ba – Gwamnatin ja

An tattaro sojojin suna cewa agajinsu aka nema da su ceci Wadume kasancewar wasu masu satar mutane ne suka sace shi, yayin da wasu rahotannin ke cewa hedikwatar 'yan sanda da ke jihar Taraba ma ba ta da labarin zuwan 'yan sandan.

Amma daga bisani 'yan sandan sun musanta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel