Yusrah: Tun Mahaifina ya na Matashi su ke tare da Gwamna El-Rufai

Yusrah: Tun Mahaifina ya na Matashi su ke tare da Gwamna El-Rufai

Bayan an tsige Malam Muhammadu Sanusi II daga kan karagar mulkin Kano, jama’a sun ga irin yadda Gwamnan Kaduna watau Nasir El-Rufai ya fito ya nuna masa goyon baya.

Nasir El-Rufai ya na cikin wadanda su ka kai wa Muhammadu Sanusi II ziyara yayin da ya ke tsare a Garin Awe a jihar Nasarawa, kuma har ya yi masa rakiya da ya bar Garin.

Wata daga cikin ‘Ya ‘yan Malam Muhammadu Sanusi, Khadijah Yusrah Sanusi ta bayyana cewa Malam El-Rufai ya yi mata bayani game da irin shakuwar da ya yi da Mahaifinta.

Yusrah Sanusi ta fito shafinta na Tuwita ta na cewa: “Yau Kawu @elrufai (Nasir El-Rufai) ya fada mani yadda shi da Mahaifina su ka taso a matsayin Abokai tun su na Matasa.”

Khadijah wanda ake yi lakabi da Yusrah ta ce: “Abokantaka ce wanda ta ratsa lokacin samu da rashi na tsawon lokaci, har zuwa tsundumawarsa aikin gwamnati cikin tsautsayi.”

KU KARANTA: El-Rufai ya ba Sanusi II mukamai a Gwamnatin Jihar Kaduna

A karshe tsohuwar Gimbiyar ta kasar Kano ta na kare jawabin na ta a shafin Tuwita da addu’a, ta na mai cewa: “Sai dai in yi addu’a Ubangiji ya hada ni da irin wannan Abokantaka.”

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta samu labari, Yusrah ta yi wannan magana ne da yammacin Ranar 14 ga Watan Maris, 2020. Wannan abu da ta fada ya jawo maganganu daga Masoya.

A wani lokacin kuma ‘Diyar tsohon Sarkin na Birnin Kano ta bayyana cewa idan Mutum ya samu Abokai irin na Mahaifinta da Gwamnan, to ba ya bukatar ya taki wata sa’a a rayuwarsa.

Mai girma Nasir El-Rufai ya maida mata amsa da cewa kowa ya na bukatar ‘yar karamar sa’a a Duniya. A karshe ya sake mika gaisuwarsa ga Mahaifinta Malam Muhammadu Sanusi II.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel