Daga karshe: El-Rufai ya koma Kaduna bayan rakiyar da ya yiwa Sanusi II zuwa Lagas

Daga karshe: El-Rufai ya koma Kaduna bayan rakiyar da ya yiwa Sanusi II zuwa Lagas

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya koma jahar Kaduna bayan ya yiwa korarren sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II rakiya zuwa jahar Lagas a daren ranar Juma’a.

Idan za ku tuna El-Rufai ya ziyarci Sanusi. Awe, jahar Nasarawa, jim kadan kafin zaman Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin daga inda aka tsare shi.

Sanusi II ya jagoranci sallar Juma’a a Awe kafin ya bar yankin cikin mota guda da El-Rufai inda suka tafi filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja don shiga kirki zuwa Lagas, bayan sun dan tsaya a gidan gwamnatin Lafiya don yin ban kwana ga Gwamnan jahar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Daga karshe: El-Rufai ya koma Kaduna bayan rakiyar da ya yiwa Sanusi II zuwa Lagas
Daga karshe: El-Rufai ya koma Kaduna bayan rakiyar da ya yiwa Sanusi II zuwa Lagas
Asali: Twitter

Yayinda ya ke Lagas, Fasto Tunde Bakare ya tarbi El-Rufai wanda ya bayyana a matsayin bikin cikarsa shekara 60 na jahar Lagas da kuma gabatar da sabon littafinsa mai suna “These Times.”

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamnan ya koma jahar Kaduna a ranar Lahadi, 15 ga watan Maris domin ci gaba da aikinsa na jan ragamar jahar.

A baya mun ji cewa Tunde Bakare ya kaddamar da littafi mai suna ‘These Times’ wanda ke kunshe da tarin jawabai da maganganun da El-Rufai ya taba yi a matsayin goron cikarsa shekaru 60 a Duniya.

Bayan wannan biki ne babban Limamin cocin na Latter Rain Assembly ya tada mutane su ka kai wa Muhammadu Sanusi II ziyara. Sai dai ba mu da labarin abin da su ka tattauna.

Fasto Bakare shi ne wanda ya tsaya takararar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a lokacin da su ke neman mulkin Najeriya a karkashin jam’iyyar CPC a 2011.

KU KARANTA KUMA: Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce

Daga cikin wadanda su ka yi wa Tunde Bakare rakiya wajen kai wa Sanusi II ziyara akwai shugabar NPA Hadiza Bala-Usman wanda ta taba rike mukami a gwamnatin El-Rufai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel