Kotu za ta saurari karar da Oshiomhole ya shigar kan dakatar dashi

Kotu za ta saurari karar da Oshiomhole ya shigar kan dakatar dashi

Kotun daukaka kara a Abuja ta dage sauraron shari’ar Shugaban jama’ iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, wanda aka shirya yi a yau Litinin, 16 ga watan Maris.

A makon da ya gabata ne kotun ta aikewa bangarorin da abun ya shafa takardar sauraron karar. Amma a lokacin da suka isa kotun a yau Litinin, sai majalisar alkalan uku karkashin jagorancin Justis Stephen Adah suka zauna sauraron sauran shari’a da ke kasa.

Daga baya sai kwamitin ta tashi, tare da alkawarin cewa za a nada wani kwamitin domin sauraron karar Oshiomhole.

Ta kuma bayyana cewa za a sanar da bangarorin sabon ranar sauraron karar.

Kotu za ta saurari karar da Oshiomhole ya shigar kan dakatar dashi
Kotu za ta saurari karar da Oshiomhole ya shigar kan dakatar dashi
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa Oshiomhole da magoya bayansa da suka isa kotun tun karfe 8:00 na safe sun shiga ganawa da lauyoyinsu kan matakin da za su dauka na gaba.

Yayinda yake barin kotun da magoya bayansa, Oshiomhole ya fada wa manema labarai cewa zai jira ya ji hukuncin kotu kan shari’ar.

KU KARANTA KUMA: Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce

Da farko dai mun ji cewa kotun daukaka kara da ke zama a Abuja a ranar Litinin, tana shirin sauraron karar da dakataccen Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole ya shigar, inda yak e kalubalantar dakatar dashi da babbar kotun Abuja ta yi.

Babbar kotun Abuja karkashin jagorancin Justis Danlami Senchi ta yi umurnin dakatar da Oshiomhole daga daukar kansa a matsayin Shugaban APC na kasa har zuwa lokacin da za a saurari karar dakatarwar da mazabarsa ta yi masa a jahar Edo.

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin da ake shiryawa taron majalisar zartarwa ta APC watau NEC, babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna cewa ya na goyon bayan Adams Oshiomhole.

Bayan dogon lokaci, Bola Tinubu ya fito ya yi magana, ya na mai sukar wadanda su ke yunkurin tunbuke Adams Oshiomhole daga kujerar da ya ke kai na shugaban APC na kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng