Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce

Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce

Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Abubakar Mahmud Gumi, ya yi martani ga tsige tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda ya yi kira ga a shafe sarautar gargajiya saboda cewa “yana mayar da mu baya.”

Gumi, wanda ya kasance Shugaban majalisar Musulman Najeriya na Shura wato MIMSA, ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da jaridar The Sun kan lamuran da ke kewaye da siyasar Najeriya, rashin tsaro da kuma garambawul.

Shehin malamin ya bayyana cewa majalisar sarakuna “tsohon yayi ne kuma ya dade da shudewa” saboda kasar Amurka da Najeriya ke bi a damokradiyarta ta shafe tsarin shekaru da dama da suka gabata.

Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce
Muhammadu Sanusi: Sheikh Gumi ya caccaki tsohon sarkin kan hawa motar Rolls Royce
Asali: UGC

Gumi ya ce tsige Sanusi bai da kowani nasaba da siyasa illa gwagwarmayar iko a arewa wanda ke ganin shugabannin yankin takura wa bangaren siyasa, inda ya yi misali da tsige tsohon Sultan na Sokoto da tsohon shugaba a mulkin soja, Sani Abacha ya yi.

Don haka malamin ya caccaki tsohon sarkin kan kasancewa munafiki. Ya ce Sanusi, wanda ya kasance tsohon gwamnan CBN, “bai kasance mai magana ba kawai, yana magana wajen fadar gaskiya rabi da rabi saboda zai fadi abu daban amma sai ya aikata wani abun daban.

“Kawai su shafe tsarin. Ya kasance tsohon yayi. Dubi yadda Gwamna Nyesom Wike ya yi wa sarakunan gargajiya a jaharsa,” in ji Gumi.

KU KARANTA KUMA: Taron NEC: Wasu Gwamnoni su na goyon bayan Shugaban APC Oshiomhole

“Dukkaninsu shirme ne. A yanzu sarautar gargajiya hukuma ce da akwai bukatar shafe ta.

“Kan Sanusi abun da zan iya karawa a gare shi shine da ba za ka kasance cikin farin ciki kana tuka motar Rolls Royce ba a lokacin da talakawanka ke cikin kangi na talauci. Da sai kada sarki Sanusi ya dunga nuna kayan alatu da kawa a tsakanin talakawansa sannan ya samu bakin yin hayaniyar da ya ke yi.

“Ka iya tuka motar Rolls Royce, amma ba ka iya biyan kudin maganin talakawanka ba. Ba sa iya ci, wasun su ma abinci sau daya a rana sannan suna kewaye dashi.”

Gumi wanda ya ce garambawul ya farad a ayyukan yan bindiga a arewa, ya ce akwai bukatar kiran taron kasa inda za a gayyaci dukkanin bangarorin da ke hanzuga su zo don tattauna matsalolin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng