Litar man fetur ya zazzago ya koma N114 – Rahotanni
Rahotanni su na zuwa mana daga Jaridar Aljazirahnews cewa farashin man fetur a kasuwa ya sauko daga kudin da gwamnati ta yi masa zuwa N114.53.
Jaridar ta bayyana cewa litar man fetur a Najeriya ta dawo N114 kamar yadda wasu Masana su ka yi hasashe a farkon watan nan na Maris saboda wasu dalilai.
Yanzu haka gangar mai ya rage farashi a kasuwannin Duniya sakamakon barkewar cutar nan ta Coronavirus wanda yanzu ta ratsa kashen Duniya fiye da 100.
A watan da ya wuce, kudin da ake sauke litar mai a Najeriya ya na kan N123.88, a dalilin haka gidajen mai ke saida fetur a kan N143.25 domin su samu riba.
Sababbin rahoton da ake samu daga hukumar PPPRA mai kula da farashin kayan mai a Najeriya ya nuna cewa yanzu kudin sauke litar mai ya koma N95.15.
A cikin ‘yan kwanaki kadan a Watan nan na Maris, litar mai ya rage kudi daga N115.52 zuwa N95.16. Ma’ana an samu ragin kusan N10 a cikin watan nan.
KU KARANTA: Tarihin karin kudin fetur a Najeriya tun daga zamanin Ironsi

Asali: UGC
Tun daga lokacin da Coronavirus ta barke a kasar China, farashin man Najeriya ya ke ta raguwa. A makon jiya an saida gangar danyen man Najeriya a kan Dala $31.
A shekarar bara sai da Najeriya ta saida danyen man ta a $67 a kasuwannin Duniya. Wannan faduwar farashi zai girgiza tattalin arzikin kasar kwarai da gaske.
Daga karshen 2019 zuwa yanzu, kudin da ake kashewa wajen sauke man da aka tace a kasar waje ya sauka da fiye da kashi 40% kamar yadda rahoton ya nuna.
A Disamban 2019, ana kashe N162.68 kafin fetur ya shigo hannun ‘yan kasuwa a gidajen mai. Wannan ya na nufin gwamnati ta na daukar nauyin tallafin mai.
Sai dai har yanzu babu labarin rage farashin mai a Najeriya. A makon jiya ne Ministan man fetur ya ce gwamnati ta na tunanin sake duba farashin man fetur.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
.
Asali: Legit.ng