Adams Oshiomhole zai san matsayar kujerarsa a Jam’iyyar APC
Manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki su na cigaba da wanke allonsu domin ganin yadda za a fita daga cikin rikicin da jam’iyyar ta fada tsamo-tsamo bayan dakatar da shugabanta.
Kamar yadda mu ka samu rahoto daga Jaridar Daily Trust, matsayar Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC ta danganta ne da hukuncin da kotu za ta yi a gobe.
Wasu ‘Yan APC su na yunkurin ganin bayan shugaban jam’iyyar na kasa, su na zarginsa da nuna karfa-karfa wajen rikon da ya ke yi wa jam’iyyar, don haka su ke neman ayi waje da shi.
Yanzu haka dai wani bangare na jam’iyyar ya kira taron NEC wanda za a yi a Ranar Talata, 17 ga Watan Maris. A daidai wannan lokaci wasu ‘yan jam’iyyar sun ce ba za ayi wannan taro ba.
A makon da ya gabata ne babban kotun tarayya ta bada umarnin cewa Kwamred Adams Oshiomhole ya dakata daga kan kujerar da ya ke rike da ita na shugaban jam’iyyar na kasa.
KU KARANTA: Gwamnoni 10 su na marawa Oshiomhole baya a tafiyar APC
Ana haka ne kuma wata kotun tarayyar ta yanke hukuncin cewa Adams Oshiomhole ya cigaba da rike mukamin na sa. Sai dai wannan hukunci da aka yi daga baya, ba zai iya shafe na farko ba.
Ana sa ran cewa a farkon makon nan ne Alkalan kotun daukaka kara na babban birnin tarayya Abuja za su raba gardama, su yanke hukunci game da wa’adin tsohon gwamnan na jihar Edo.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Yankin Arewa maso Gabas, Mustafa Salihu, da shugaban APC na Mazabar Etsako a jihar Edo, Steven Oshawo su na cikin wadanda su ka kai kara kotu.
Magoya bayan Oshiomhole irinsu Henry Idahagbon su na ganin cewa kotun daukaka kara za ta ba shugaban jam’iyyar da aka dakatar gaskiya, a ganinsa dakatarwar na gajeren lokaci ne kurum.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng