Tinubu ya bayyana matsalar da ke barazanar kashe APC kamar yadda 'Corona Virus' ke kashe mutane

Tinubu ya bayyana matsalar da ke barazanar kashe APC kamar yadda 'Corona Virus' ke kashe mutane

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya ce burin takarar shugaban kasa na wasu manyan 'yan siyasa yana barazanar lalata jam'iyyar APC kamar annobar bullowar 'Coronavirus'.

A cikin jawabin da ya fitar ranar Lahadi, Tinubu ya bayyana cewa abin takaici ne cewar har ta kai ga masu wannan buri sun kitsa dakatar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

"Duk da mun samu nasarar dakile yaduwar 'coronavirus' a cikin Najeriya, akwai bukatar mu tashi tsaye domin magance wata cutar da take neman zama ruwan dare a tsakanin wasu tsirarun mutane. Wannan cuta ita ce kwayar cutar burin samun takarar shugaban kasa a 2023. Wannan cuta, yanzu haka, ta kama wasu manyan 'yan siyasa da 'yan barandarsu a kafafen yada labarai," a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa, "masu fama da wannan kwayar cuta sun shiga cikin dimuwa, saboda sun gaza fahimtar banbancin da ke tsakanin yanzu d kuma gobe. Sun shiga rudani kwatankwacin irin wanda kasarmu ta tsinci kanta a halin yanzu.

Tinubu ya bayyana matsalar da ke barazanar kashe APC kamar yadda 'Corona Virus' ke kashe mutane

Tinubu
Source: Facebook

"Su kadai ke yin irin tunanin da suke yi. Ta yadda za a gane cewa sun kamu da kwayar cutar burin takarar shugaban kasa, shine ta yadda suke kokarin yanke shawara a kan abinda zai faru a 2023 tun bamu fita daga shekarar 2020 ba.

DUBA WANNAN: Fansho da albashi: SERAP ta fitar da sunayen tsofin gwamnoni da ke cin 'tudu biyu' a asusun Najeriya

A cewar tsohon gwamnan na jihar Legas, babban abin takaicin shine yadda shugaba Buhari ke shan wahala da jin jiki sakamakon halayyar wadancan mutane da cutar burin takara a 2023 ta kama.

Tinubu, ya ce kamata ya yi duk 'yan jam'iyyar APC su bawa shugaba Buhari hadin kai da goya masa baya a kokarinsa na magance matsalolin da kasa ke fama da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel