Tsige Sarki: Allah ya rubuta ba zan kara kwana guda bayan 9 ga Maris ba inji Sanusi

Tsige Sarki: Allah ya rubuta ba zan kara kwana guda bayan 9 ga Maris ba inji Sanusi

A wani bidiyo da ya ke yawo yanzu a kafafen yada labarai, an ji tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya na bayani game da tunbuke shi da aka yi daga kan karagar mulki a Kano.

A wannan bidiyo, Sanusi II ya bayyana cewa ana tunbuke shi daga kan mulki, ya fara tunanin dawowa Legas domin nan ne tamkar gida inda ya tashi kuma ya girma da Abokansa.

Malam Muhammadu Sanusi II ya nuna cewa ya rungumi kaddara, har ya ke bada labarin yadda babbar ‘Diyarsa ta fashe da kuka yayin da ta hadu da shi a filin jirgi bayan an sauke shi.

A jawabin da ya yi a gidan da ya zauna a Garin Awe, Nasarawa, Muhammadu Sanusi II ya ce a danginsu, sun yarda cewa Ubangiji ne ya ke bada mulki, kuma ya karbe idan har ya so.

Wannan tawakalli na Malam Sanusi II ya sa ya nunawa ‘Diyasa cewa Ubangiji bai nufa cewa zai kara kwana daya a kan gadon sarautar Kano bayan Ranar 9 ga Watan Maris, 2020 ba.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya halarci sallar Juma’ar farko bayan nada sabon Sarki

Tsige Sarki: Allah ya rubuta ba zan kara kwana guda bayan 9 ga Maris ba inji Sanusi
Malam Muhammadu Sanusi II ya koma Legas bayan an cire masa rawani
Asali: Twitter

Sanusi II ya tunawa jama’an da su ka kawo masa ziyara a wancan lokaci da cewa ya rike shugaban babban bankin First Bank, sannan ya zama gwamnan CBN, kuma ya rike Sarki.

Tsohon Sarkin na Birnin Kano ya ce babu abin da zai tsaya a rayuwarsa bayan an tube masa rawani, ya ce zai halarcin bikin da aka gayyacesa a Jami’ar Legas a karshen watan nan.

Haka zalika tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar ya nuna cewa zai cigaba da aikin babbar gona da sauran shirye-shirye da tsare-tsaren da ya ke jagoranta irinsu SDG da sauransu.

A cewarsa, abin da zai canza a rayuwarsa shi ne yanzu ba ya gadon sarauta sai kuma hawa doki, wanda shi ma ya yi shekara da shekaru ya na yi, ya nuna cewa mulki bai tsone masa ido ba.

Malam Sanusi II ya ke cewa ya godewa Ubangiji da damar da ya samu, kuma a karshe ya na alfahari cewa za a ce shi Sarki ne na mutanen Kano ba Sarkin gwamnatin Jihar Kano ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel