Yadda sallolin Juma’an farko su ka kasancewa sababbin Sarakunan Kano da Bichi

Yadda sallolin Juma’an farko su ka kasancewa sababbin Sarakunan Kano da Bichi

A Ranar Juma’ar nan da ta wuce ne mu ka samu labarin cewa Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya gabatar da sallar juma’a ga Talakawansa.

Sabon Sarkin da aka nada watau Nasiru Ado Bayero ya yi wa mutanen Garin Bichi sallah ne tare da gabatar da hudubar Juma’a a Ranar 13 ga Watan Maris, 2020.

Mai martaba Nasiru Bayero ya gabatar da wannan sallah ne a babban masallacin Juma’a da ke Garin Bichi kamar yadda mu ka samu labari daga kafafen sadarwa.

Shafin masarautar Bichi a dandalin sada zumunta na Tuwita su ka wallafa hotuna da bidiyoyi na yadda bikin Juma’ar ta kasancewa sabon Sarkin na kasar Bichi.

Bayan an idar da sallah, Sarkin ya fito a kan doki har zuwa gidansa inda Dadawa da Dogarai da sauran Jam’an Gari su ka rika yi wa sabon Sarkin na su jinjina.

KU KARANTA: Buhari ya yi kokarin ganin Sanusi II ya cigaba da rike sarautar Kano

A cikin birnin Kano kuma sabon Sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci sallar da aka yi ne a babban masallacin Sarki. Sai dai ba Sarkin ba ne ya yi limanci a nan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Darekta Janar na yada labarai a gidan gwamnatin jihar Kano, Farfesa Sani Zahraddeen ne ya yi limacin Juma’a a masallacin Sarki.

Salihu Tanko Yakassai ya bayyana wannan a shafinsa na Tuwita inda ya taya babban Limamin dawowa kan mimbarin da ya saba gabatar da sallar Juma’a a Kano.

A lokacin Muhammadu Sanusi II ya na kan karagar mulki, ya kan jagoranci sallar Juma’a da huduba cikin harshen larabci. Da alamu an sake canza wannan al’ada.

Daga cikin wadanda su ka halarci sallar Juma’ar da aka yi a masallacin Sarkin Birni har da Mai girma gwamnan jihar Kano, Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel