Tunde Bakare ya jagoranci Jama’a gaban tsohon Sarkin Kano da aka tsige

Tunde Bakare ya jagoranci Jama’a gaban tsohon Sarkin Kano da aka tsige

Kwanaki kadan da tsige Muhammadu Sanusi II daga kan karagar sarautar Birnin Kano, wasu manya da ake ji da su, su na ta cigaba da kai wa Malam Muhammadu Sanusi II ziyara.

Labari ya zo mana cewa gwamnan jihar Kaduna, Mai girma Malam Nasir El-Rufai ya sake ganawa da tsohon Sarkin da gwamnatin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke.

El-Rufai wanda ya na tare da tsohon Sarkin a lokacin da ya ke tsare a Nasarawa har zuwa filin jirgin Abuja domin yi masa rakiyar tafiya Legas a Ranar Juma’a, ya sake ganawa da shi.

Fasto Tunde Bakare shi ne wanda ya jagoranci Nasir El-Rufai da wasu zuwa wajen Muhammadu Sanusi II. An yi wannan ne kwana guda da tarewar tsohon Sarkin na Kano a Garin Legas.

Kamar yadda shafin Tuwita na gwamnatin jihar Kaduna ya bayyana, an yi wannan zama ne jim kadan bayan Tunde Bakare ya kaddamar da wani littafi da sunan Malam Nasir El-Rufai.

KU KARANTA: Na san za a tsige Muhammadu Sanusi II - Ahmed Joda

Tunde Bakare ya jagoranci Jama’a wajen tsohon Sarkin Kano da aka tsige
Tsohon Sarkin Kano Sanusi II, El-Rufai, da Hadiza Usman
Asali: Twitter

Tunde Bakare ya kaddamar da littafi mai suna ‘These Times’ wanda ke kunshe da tarin jawabai da maganganun da El-Rufai ya taba yi a matsayin goron cikarsa shekaru 60 a Duniya.

Bayan wannan biki ne babban Limamin cocin na Latter Rain Assembly ya tada mutane su ka kai wa Muhammadu Sanusi II ziyara. Sai dai ba mu da labarin abin da su ka tattauna.

Fasto Bakare shi ne wanda ya tsaya takararar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a lokacin da su ke neman mulkin Najeriya a karkashin jam’iyyar CPC a 2011.

Daga cikin wadanda su ka yi wa Tunde Bakare rakiya wajen kai wa Sanusi II ziyara akwai shugabar NPA Hadiza Bala-Usman wanda ta taba rike mukami a gwamnatin El-Rufai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel