‘Dan Isa da ‘Dan Majen Zazzau sun kai wa Aminu Bayero gaisuwa a Kano

‘Dan Isa da ‘Dan Majen Zazzau sun kai wa Aminu Bayero gaisuwa a Kano

Yayin da Mai martaba Aminu Ado Bayero ya ke cigaba da gyara zama a kan karagar Sarkin Birnin Kano, jama’a su na ta kara yi masa mubaya’a a fadarsa.

Kamar yadda mu ka samu labari, a jiya Ranar Asabar, 14 ga Watan Maris, 2020, wata Tawaga daga Birnin Zazzau ta tashi zuwa Kano domin nuna farin cikinta.

‘Dan Isan Zazzau, Umar Shehu Idris da kuma ‘Dan Majen Zazzau, Nasiru Shehu Idris, sun kai ziyarar ban girma ga sabon Sarkin Birnin Kano a jiya Asabar.

Mun samu wannan labari ne daga wani shafi na Masoya Mai martaba Aminu Ado Bayero da ke kan dandalin sada zumunta na zamani watau Twitter dazu.

Rahotanni sun bayyana mana cewa ‘Dan Isan Zazzau da danuwansa‘Dan Majen na Zazzau sun kawowa Aminu Bayero ziyara ne domin jaddada mubaya’arsu.

KU KARANTA:

‘Dan Isa da ‘Dan Majen Zazzau sun kai wa Aminu Bayero gaisuwa a Kano
Mai martaba Alhaji Aminu Bayero a kan kujerar Mahaifansa
Asali: Twitter

Bayan haka kuma manyan ‘Ya ‘yan Sarkin na Zazzau sun kuma kawowa Aminu Bayero sakon taya murnar Mahaifinsu Mai martaba Alhaji Shehu Idris.

Shehu Idris wanda yanzu ya shafe shekaru 45 a kan mulkin Zazzau ya kasance Abokin tsohon Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu a 2014.

Idan ba ku manta ba lokacin da aka nada Aminu Bayero Sarki a kasar Bichi, manyan masu rike da sarauta a kasar Zazzau sun garzaya sun taya sa murna.

Haka zalika a Ranar Juma’ar da ta gabata, sabon Sarkin ya karbi gaisuwa Juma’a daga mutane da-dama wadanda su ka nuna goyon bayansu ga Mai martaba.

Ku na sane cewa Aminu Ado Bayero ya dare kan kujerar Iyayensa ne bayan gwamnatin jihar Kano ta tsige Muhammadu Sanusi II bisa ga laifin rashin da’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel