Har yanzu Sanusi ne shugaban gudanarwa na jami'ar Ekiti - Shugaban Jami'a

Har yanzu Sanusi ne shugaban gudanarwa na jami'ar Ekiti - Shugaban Jami'a

Hukumar gudanarwa ta jami’ar jihar Ekiti (EKSU) da ke Ado Ekiti, ta ce har yanzu dai tubabben sarki Sanusi Lamido II ne shugaban gudanarwa na jami’ar duk kuwa da tube masa rawani da aka yi.

An tubewa tsohon sarkin rawani ne a ranar Litinin sakamakon zarginsa da rashin biyayya daga gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Kayode Fayemi ne ya nada Sanusi Lamido matsayin shugaban gudanarwar jami’ar a shekarar 2019.

A wasikar da jami’ar ta fitar a ranar 12 ga watan Maris na 2020 wacce shugaban makarantar, Farfesa Eddy Olanipekun yasa hannu kuma aka mika ta ga tsohon sarkin, ya ce jami’ar har a halin yanzu tana nan rike dashi a matsayin shugaban gudanarwarta duk da halin da ake ciki yanzu.

Har yanzu Sanusi ne shugaban gudanarwa na jami'ar Ekiti - Shugaban jami'a

Har yanzu Sanusi ne shugaban gudanarwa na jami'ar Ekiti - Shugaban jami'a
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sanusi II zai shugabanci lakca din yayen dalibai a LASU

Wasikar kamar yadda ta bayyana, ta ce wannan hukuncin ya biyo bayan hazaka, ilimi da kuma gogewar tsohon sarkin wanda yake matukar amfanar jami’ar wajen tabbatar da ci gabanta.

Jami’ar wacce ta jajantawa sarkin a kan yadda aka sauke masa rawani, ta ce har abada irin salon mulkin sarkin zai zama abin tunawa da koyi a tarihin masarautar Kano.

Kamar yadda wasikar ta bayyana: “Har yanzu kaine shugaban gudanarwa ta jami’ar nan sakamakon amincewa da sakankancewa da muka yi da gogewarka wacce babu shakka tana amfanar jami’ar. Labarin sauke maka rawani ya matukar gigiza jami’ar kuma hakan yasa muka kara tabbatar da cewa Ubangiji kadai ke bada mulki tare da kwacesa daga hannun wanda yaso.”

“Jami’ar na jinjina maka ta yadda ka yi iyakar kokarinka a karantaccen lokacin da ka hau karagar. Hukumar gudanarwa, shugabanni, ma’aikata da kuma daliban EKSU suna tare da kai a wannan lokacin na jarabawa a rayuka. Muna sake tabbatar maka da goyon bayanmu a yayin da kake komawa sabuwar rayuwa,” wasikar ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel