Yanzun nan: An tsaurara matakan tsaro a Awe yayinda Sanusi ke shirin bayyana a cikin jama’a don sallar Juma’a

Yanzun nan: An tsaurara matakan tsaro a Awe yayinda Sanusi ke shirin bayyana a cikin jama’a don sallar Juma’a

Rahotanni sun kawo cewa an tsaurara matakan tsaro a garin Awe na jahar Nasarawa, inda aka ajiye korarren sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II tun bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya tsige shi.

An gano jami’an rundunar sojin Najeriya, jami’an tsaro na yan sandan fari n kaya (DSS), yan sanda da kuma jami’an hukumar Civil Defence zube wadanda ke bayar da kariya ga tsigaggen sarkin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai a wata hira da kwamishinan yan sandan jahar, Bola Longe, ya ce an zuba matakan tsaro ne a karamar hukumar Awe na jahar Nasarawa domin amfanin kowa.

Yanzun nan: An tsaurara matakan tsaro a Awe yayinda Sanusi ke shirin bayyana a cikin jama’a don sallar Juma’a
Yanzun nan: An tsaurara matakan tsaro a Awe yayinda Sanusi ke shirin bayyana a cikin jama’a don sallar Juma’a
Asali: Facebook

"An zuba Karin jami’an tsaro ne a garin domin su kare mazauna yankin da baki a garin, ba wai don tsorata kowa ba.

“Ina rokon mutanen Awe masu halin kirki da su bi oda musamman a lokacin sallar Juma’a,” in ji CP Longe a ranar Alhamis.

An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaro a garin ne saboda bayyanar da Sanusi zai yi a sallar Juma’a domin jam’i da sauran Musulmai.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya kai ma Malam Muhammadu Sunusi II ziyara a Awe

An kuma lura cewa jami’an EOD na ta duba motoci da ke tunkarar gidan da kuma hana masu motocin kasuwa bin kofar gidan.

A halin da ake ciki, munn ji cewa abban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga inda aka tsare shi a garin Awe na jihar Nasarawa bayan an cire daga kan mulki a ranar Litinin.

Mai shari'ar Anwuli Chikere ne ta bayar da umurnin sakamakon bukatar da shugaban lauyoyinsa, Latee Fagbemi (SAN) ya shigar a ranar Juma'a.

Kotun ta ce a mika takardan umurnin sakin Sanusi da dukkan hukumomin da suka tsare da shi.

Wadanda Sanusi ya yi karar su a kotun kan batun tsare shi suna hada da Sifeta Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi; Attony Janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da Ministan Shari'a na Najeriya, Mista Abubakar Malami (SAN).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel