Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero

Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero

Wasu kyawawan tsoffin hotunan korarren sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido da uwargidarsa Sadiya Ado Bayero ya billo yayinda suka yi fice a shafukan intanet.

Koda dai ba kowa bane ya san cikakken labarin matar tsohon sarkin na farko, hujja ya nuna cewa ta fito ne daga gidan sarautar Kano.

A bisa ga rahotanni, Sadiya ta kasance ‘yar uwar Sanusi Lamido. Ita ce ya mace ta bakwai kuma ta 16 a wajen marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, kuma kanwa ce ga sabon sarkin Kano mai ci, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya karbi mulki daga hannun korarren mijinta.

Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero

Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero
Source: UGC

Ma’auratan sun fara soyayya a lokacin da suke matasa sannan suka yi aure a zamanin 80s, inda aka yi biki irin na Fulani.

A wani hira da Sadiya ta taba yi da wata mujallar Hausa mai suna Aminiya a yan shekaru da suka gabata, ta bayyana cewa ta hadu da mijinta ne ta ahlinta. Ta bayyana cewa kamar ‘ya’ya yake a wajenta domin ya taso ne a fadar sarki.

Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero

Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Sanusi na rayuwa tamkar dan fursuna yayin da yan sanda da NSCDC suka hana baki ganinsa - Rahoto

Kyawawan ma’auratan sun yi aure sama da shekaru ashirin da suka wuce sannan kuma da aka tambayi Sadiya kan yadda aka yi ta dade a aure haka da mijinta wanda ya kasance shahararre, ta bayyana cewa hakuri da biyayya ne ya taimake ta duk da matsayinta.

Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero

Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero
Source: UGC

A wani labari na daban, mun ji cewa A yanzu haka ana nan ana ci gaba da ginin gidan da aka ajiye korarren sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a karamar hukumar Awe, da ke jahar Nasarawa, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Laraba, 11 ga watan Maris, an gano ma’aikata na ta kai wa da komowa domin kimtsa gidan wanda ke kimanin mita 500 daga fadar sarkin Awe.

An gano masu sanya wayoyin lantarki da fentin ginin na ta aiki ba kakkautawa. Sannan kuma wata babbar mota na ta kawo yashi domin kammala ginin cikin gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel