Har yanzu ana kan ginin sabon muhallin Sanusi II, ana kan yin fenti

Har yanzu ana kan ginin sabon muhallin Sanusi II, ana kan yin fenti

A yanzu haka ana nan ana ci gaba da ginin gidan da aka ajiye korarren sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a karamar hukumar Awe, da ke jahar Nasarawa, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Laraba, 11 ga watan Maris, an gano ma’aikata na ta kai wad a komowa domin kimtsa gidan wanda ke kimanin mita 500 daga fadar sarkin Awe.

An gano masu sanya wayoyin lantarki da fentin ginin na ta aiki ba kakkautawa. Sannan kuma wata babbar mota na ta kawo yashi domin kammala ginin cikin gidan.

Umar Tanko Akano, Shugaban karamar hukumar Awe ne dai ya mallaki gidan da aka ajiye tsohon sarkin Kanon a Awe.

Har yanzu ana kan ginin sabon muhallin Sanusi II, ana kan yin fenti

Har yanzu ana kan ginin sabon muhallin Sanusi II, ana kan yin fenti
Source: Facebook

“An dade da gina gidan, amma ba a kammala ba kuma ba kasafai ake amfani dashi ba. Amma tunda Sanusi ya zo nan, ana ta wasu ayyuka kamar yadda kuke gani a yanzu,” cewar Mamman Mohammed wani mutum da ke zama yan kilomita kadan daga gidan.

An dauko Sanusi wanda aka tsige daga matsayin sarkin Kano a ranar Litinin daga masarautarsa zuwa Abuja sannan aka garzaya dashi Loko a jahar Nasarawa.

Daga Loko, aka dauke shi zuwa Lafia, sannan aka kais hi Awe, wanda aka ce nan ne muhallinsa har sai baba ya gani.

Wasu mazauna yankin sun ce sun ji cewa Sanusi zai zauna a gidan na tsawon akalla watanni uku.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari ya umurci El-Rufai ya baiwa Sanusi Lamido mukami

Awe wani dan karamin gari ne a kudancin Lafia. Kimanin kilomita 85 daga babbar birnin jahar Nasarawa.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano da aka tsige, na nan yana rayuwa tamkar dan gidan yari tun bayan da aka kai shi karamar hukumar Awe da ke jahar Nasarawa.

A cewar mazauna yankin, an hana wasu mutane da suka kai ziyara ganin Sanusi wanda aka dauke daga Kano a yammacin ranar Litinin, jaridar The Cable ta ruwaito.

An rahoto cewa akalla jami’an yan sanda da na NSCDC 30 ne ke gadin sabon muhallin tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya (CBN).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel