Haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a Jami'o'i – Inji Chris Ngige

Haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a Jami'o'i – Inji Chris Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyukan Najeriya, Dr. Chris Ngige, ya yi magana game da sabanin da gwamnatin tarayya ta samu da kungiyar ASUU ta Malaman Jami’o’i.

Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a dalilin tursasawa ‘Ya ‘yanta shiga cikin tsarin albashin nan na IPPIS da aka kawo.

Dr. Ngige ya yi maganar ne a fadar shugaban kasa bayan an kammala taron FEC a Ranar Laraba. Wannan ne karon farko da gwamnati ta yi magana game da yajin kungiyar.

Da ya ke amsa tamboyoyin ‘Yan jarida, Ngige ya ce kungiyar ASUU ba ta sanar da gwamnatin tarayya halin da ta ke ciki ba, sai kurum ta tafi yajin aikin makonnni biyu.

A cewar Ministan kwadagon, ya na daga cikin rashin gaskiya ace an biya masu yajin aiki albashi domin kuwa ba su yi gumin komai ba a lokacin da su ka kauracewa ofisoshinsu.

KU KARANTA: Malaman Jami’an Gwamnatin tarayya sun fara yajin aiki a Najeriya

Haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a Jami'o'i – Inji Chris Ngige
ASUU sun fara yajin aiki a Najeriya a kan batun shiga tsarin IPPIS
Asali: Facebook

Ministan kasar ya bayyanawa Manema labarai cewa Ma’aikatarsa ta shirya zama da ‘Yan ASUU a Ranar Alhamis domin shawo kan sabanin da ya shiga tsakaninsu da gwamnati.

Ngige ya nuna cewa an jima kadan kungiyar ASUU za ta zauna da shi da Ministan ilmi, da Ministar kudi da tattali da kuma babban akantan Najeriya domin samun mafita.

Ko da Ministan ya na sa ran cewa gwamnatin Najeriya za ta shawo kan wannan yajin aiki, sai dai ya ce babu ma’aikacin da ya isa ya fadawa gwamnati yadda za a biyasa albashi.

Mai girma Ministan ya na ganin yajin aikin da ASUU ta shiga bai halatta ba. Gwamnati dai ta dakatar da biyan albashin wadanda su ka guji IPPIS ne saboda rage facakar kudi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng