Gudun hijira: Iyalin Muhammadu Sanusi II sun kai masa ziyara a Garin Awe

Gudun hijira: Iyalin Muhammadu Sanusi II sun kai masa ziyara a Garin Awe

Daya daga cikin Matan tsohon Sarkin Birnin Kano, Muhammadu Sanusi, ta kai masa ziyara a sabon gidan da ake yi masa daurin talala a Garin Awe, Nasarawa.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Iyalan tsohon Sarkin sun kawo masa ziyara ne da safe wajen kimanin karfe 11:00. Har da wasu ‘Ya ‘yan Sanusi II a cikin Tawagar.

Rahotanni sun ce Iyalin tsohon Sarkin na Kano sun zo ne a cikin wata katuwar bakar mota kirar SUV wanda aka toshe ta yadda ba a iya ganin mutanen da ke cikinta.

Haka zalika an samu Jami’an tsaron ‘Yan Sanda da hukumar DSS masu fararen kaya dauke cikin wata motar Toyota Hilux su na yi wa Iyalin tsohon Sarkin rakiya a baya.

Jaridar ta bayyana cewa wadannan motoci su na dauke ne da lambar gidan gwamnatin jihar Kaduna. Akwai alamun cewa akwai hannun gwamnan jihar a ziyarar.

KU KARANTA: Muhammadu Sanusi ya taya sabon Sarkin Kano murnar samun sarauta

Gudun hijira: Iyalin Muhammadu Sanusi II sun kai masa ziyara a Garin Awe
Wasu daga cikin Iyalin Sanusi II da ke Legas sun kawo masa ziyara
Asali: UGC

Idan ba ku manta ba, daga lokacin da aka tunbuke Muhammadu Sanusi II daga kan sarauta, gwamnatin Nasir El-Rufai ta ba shi manyan mukamai biyu a jihar Kaduna.

Wasu daga cikin ‘Ya ‘yan Muhammadu Sanusi II su uku sun samu ganawa da Mahaifin na su a wannan ziyara da su ka kawo masa a Garin Awe da ke jihar Nasarawa jiya.

Mai martaba Sarkin Awe, Alhaji Umar Isa Abubakar da Takawaransa Sarkin Azara, Dr. Kabir Musa Ibrahim su na cikin wadanda su ka gana da Muhammadu Sanusi II.

Tsohon Mai martaban duk ya yi wannan ganawa ne da jama’a a jiya Ranar Laraba, 11 ga Watan Maris. Sai dai Jami’an tsaro ba su barin sauran jama’a su iya ganinsa a gidan.

Kamar yadda mu ka samu labari akalla Dakarun Jami’an tsaro 40 ke gadin gidan da ake tsare Sanusi II. Wannan gida ya na bakin titi ne a kan hanyar zuwa Garin Benuwai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel