Wani mutumi ya bi daliba da abokananta suke yi mata dariya saboda kayan makarantar ta sunyi mata yawa ya dinka mata sabo

Wani mutumi ya bi daliba da abokananta suke yi mata dariya saboda kayan makarantar ta sunyi mata yawa ya dinka mata sabo

- Wani mutumi ya je har makarantar su wata yarinya da yaga an sanyata a shafin sadarwa wacce kayan ta suka yi mata yawa

- Mutumin ya siya mata sabon kayan makaranta ya dinka mata sannan ya kai mata makaranta

A ranar Talata 21 ga watan Janairu, Gauteng Survivors ta kawo rahoton wani mutumi mai kirki wanda suka bayyana sunanshi da Gavin Khalima Khungwayo.

A 'yan kwanakin da suka gabata shafukan sadarwa sun cika da labarai na komawar yara dalibai makaranta bayan shafe tsawon lokaci suna hutu a gida.

Wata yarinya karama da aka fi magana a kanta, wacce rashin wadata ya sanya iyayenta suka tilasta ta komawa makarantar da kaya wadanda suka yi mata yawa sosai.

Yarinyar na shan dariya da zolaya a wajen 'yan uwanta dalibai akan wannan kayan makaranta da take sanyawa.

Khungwayo yayi tunanin cewa idan ya taimaka mata hakan zai kawo karshen tsokanarta da 'yan uwanta dalibai suke yi mata.

Mutumin yayi amfani da kudin shi wajen sayo mata sabon kayan makaranta ya kuma nemo makarantar da dalibar take, ya bata wadannan kaya, sannan ya dauketa aka yi musu hoto tare.

KU KARANTA: Wani kare da baya iya tafiya ya fara kawance da wata tattabara da ba ta iya tashi

Fuskar yarinyar ta fara samun fara'a bayan ganin irin wannan abu da Khungwayo yayi mata na kyautatawa.

Wannan abu da yayi ya sanya mutane da dama mamaki a shafukan Twitter da Facebook, da yawa suka dinga yi masa godiya da sanya albarka akan wannan abu da yayi, kuma suke rokon Allah yasa sauran mutane su cigaba da koyi da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel