Mun karbo N3.7b da su ka yi kafa a hukumar Neja-Delta Inji Buhari

Mun karbo N3.7b da su ka yi kafa a hukumar Neja-Delta Inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jami’an tsaron Najeriya sun gano kudin da su ka haura Naira biliyan 3.7 a hannun ‘yan kwangila da wasu tsofaffin jami’an hukumar NDDC.

Kamar yadda mu ka samu labari shugaban kasar ya bayyana cewa an yi nasarar karbo wasu daga cikin wannan makudan kudi ne wajen kaddamar da wani kwamiti na ma’aikatar Neja-Delta.

Wannan kwamiti da aka kafa ya kunshi gwamnonin Yankin da ke da mai a Kudancin kasar da kuma Ministocin muhalli da na harkokin Neja-Delta. Ministan N/Delta zai jagoranci kwamitin.

Buhari ya fada masu cewa:

Kawo yanzu, EFCC da sauran hukumomi da ke bincike sun gano tsabar kudi Biliyan N3.7 tare da wasu kadarorin Naira biliyan uku daga ‘yan kwangila da kuma wasu tsofaffin ma’aikata.”

“Bayan haka an fada mani cewa hukumomi su na bincike kan wasu kadarorin na Naira biliyan 6.” Ana zargin wasu wadanda su ka rike mukamai a Neja-Delta da tafka wannan badakala.

KU KARANTA: Ayyukan da Buhari zai yi wa Najeriya da bashin da zai karbo

Mun karbo N3.7b da su ka yi kafa a hukumar Neja-Delta Inji Buhari

Buhari ya dage da bincike kan barnar da ake yi a hukumar NDDC
Source: Twitter

A 2016 ne gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin ‘New Vision for the Niger Delta (NEVIND)’ domin inganta muhalli da tsaro da rayuwar mutanen Neja-Delta, sai dai ba ayi nasara ba.

“A dalilin wannan ne a Fubrairu na sake kafa kwamitin mutum 10 da zai taya shugaban kasa lura da harkokin Neja-Delta kamar yadda sashe na 21 na dokar da ta kafa NDDC ta zayyana.”

Shugaban kasar ya tunawa kwamitin cewa: “A zaman FEC na Ranar 5 ga Watan Fubrairun 2020 mu ka amince da kawo masu binciken kudi da za su bi diddikin ayyukan hukumar NDDC."

Gwamnatin Buhari duk ta kawo wannan tsare-tsare ne domin kawo karshen satar dukiya da ake yi a maimakon yi wa Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur ayyuka na more rayuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel