Badakala: An mika sunayen hadiman Ganduje 11 ga kotun CCTB

Badakala: An mika sunayen hadiman Ganduje 11 ga kotun CCTB

Kasa da wata daya bayan hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzki (EFCC) ta kama kwamishinan harkoki na musamman a Kano, Mukhtar Ishaq Yakasai, bisa zarginsa da almundahanar kudi, N86m, an sake samun wasu hadiman gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da laifi mai nasaba da bayyana kadarori.

A cewar wani bincike da PRNigeria ta gudanar, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa, an samu hadiman 11 da laifin kin bayyana zahirin kudi da ke cikin asusunsu da kuma kadarorin da suka kamar yadda doka ta tanada.

A cewar Daily Nigerian, PRNigeria ta hango sunan babban darektan yada labaran gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, a matsayin na farko a cikin jerin hadiman gwamnan da za a tuhuma da laifin kin bayyana kadarorinsu bisa tsarin dokokin ma'aikata da jami'an gwamnati.

Sauran hadiman gwamna Ganduje da sunayensu ke cikin takardar sun hada da; Uba Tanko Mijinyawa (mataimaki na musamman a kan sabbin kafafen watsa labarai), Injiniya Mansur Ahmed (mataimaki na musamman a kan aiyuka na musamman), Tanko Indi Sarki, Ado Abba Tudun Wada (babban darektan harkokin matasa) da Kabiru Baita (mataimaki na musamman a bangaren wasanni).

Badakala: An mika sunayen hadiman Ganduje 11 ga kotun CCTB
Salihu Yakasai da Ganduje
Asali: Twitter

A cewar rahoton, wasu hadiman Ganduje guda hudu sun ki bawa dokar bayyana kadarori hadin kai, hadiman sune; Habibu Saleh (mataimaki na musamman a kan kudin shiga), Saleh Shehu K (mataimaki na musamman a kan hanyoyin samun kudin shiga na cikin gida), Zulyadaini Sidi Mustapha (mataimaki na musamman a kan SDGs) da Haruna D. Zago (mataimaki na musamman a kan tsaftar abinci).

Sai dai, PRNigeria ta bayyana cewa hukumar tabbatar da da'ar ma'aikata (CCB) na fuskantar matsin lamba daga manyan hadiman gwamnan da sauran jami'an gwamnatin Ganduje domin ganin sunayensu basu kai ga kotun da'ar ma'aikata (CCT) ba, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

DUBA WANNAN: Da sauran tsalle: Hukumar yaki da cin hanci a Kano za ta cigaba da tuhumar Sanusi II

Amma wata majiya a hukumar CCB ta bayyana cewa tuni an kammala hada sunayen hadiman domin aika su zuwa kotun CCT da ke karkashin alkalin nan da ba ya wasa, wato Jastis Danladi Umar.

Hukumar CCB ce ta farko da aka kafa a Najeriya domin yaki da cin hanci a tsakanin ma'aikatan gwamnati.

An kafa hukumar ne tare da kotun CCT domin gurfanar da duk wani ma'aikaci da aka samu da laifin almundahana ko almubazzaranci da kudin hukuma da sauran wasu laifuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng