Yanzu Yanzu: Sabbin sarakunan Kano da Bichi na shirin karban takardun nadinsu

Yanzu Yanzu: Sabbin sarakunan Kano da Bichi na shirin karban takardun nadinsu

- Sabon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero zai amshi takardar nadinsa a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, a dakin nadin sarauta da ke jahar

- Hakazalika sabon sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ma zai karbi takardar nadinsa a wajen taron da misalin karfe 4:00 na rana

- Gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta nada sarakunan, wadanda suka kasance yaya da kani kuma yaran marigayi sarkin Kano, Ado Bayero

Kwanaki biyu bayan kaddamar dashi a matsayin sabon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero zai amshi takardar nadinsa a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, a dakin nadin sarauta da ke jahar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa sabon sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ma zai karbi takardar nadinsa a wajen taron da misalin karfe 4:00 na rana.

Yanzu Yanzu: Sabbin sarakunan Kano da Bichi na shirin karban takardun nadinsu
Yanzu Yanzu: Sabbin sarakunan Kano da Bichi na shirin karban takardun nadinsu
Asali: UGC

Gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta nada sarakunan, wadanda suka kasance yaya da kani kuma yaran marigayi sarkin Kano, Ado Bayero bayan tsige tsohon sarki Muhammadu Sanusi II kan zargin rashin mutunta al’adun birnin mai tsohon tarihi.

KU KARANTA KUMA: An tsaurara tsaro a sabon gidan Muhammadu Sanusi II da ke Awe

Idan za a tuna a ranarTalata ne sabon Sarkin Kano, Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance a gidan sarki da ke Nassarawa don yin adu’o’i ga mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero.

Sabon Sarkin ya kara da garzayawa zuwa wajen mahaifiyarsa da ke unguwar Gandun Albasa domin neman tabaraki garesa da sauran hakiman Kano da suka yi mubaya’a.

Ya kara da biyowa ta titin gidan Zoo daga nan ya wuce gidansa da ke Mandawari duk a cikin birnin Kanon.

Kamar yadda gidan rediyon Freedom da ke Kano ta ruwaito, jama’ar jihar Kano da kuma jami’an tsaro ne suka raka sabon sarkin wajen mahaifiyarsa.

A ranar Talata, 10 ga watan Maris ne al'ummar Kano da dama suka yi tururuwa zuwa gidan sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero domin taya shi murnar nadin da aka masa a matsayin sarki. Mutanen sun isa gidan suna kirari da wakoki na murnar nada sabon sarki a Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng