Ana sa rai yau za a mikawa sabon Sarkin Birnin Kano Bayero sandar-girma

Ana sa rai yau za a mikawa sabon Sarkin Birnin Kano Bayero sandar-girma

Watakila sabon Sarkin birnin Kano watau Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, ya karbi sandar girmar shiga ofis a Yau Laraba, 11 ga Watan Maris, 2020.

Tun a jiya Ranar Talata aka sa ran cewa sabon Sarkin zai karbi sandar girmar kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana, sai dai har yanzu hakan bai faru ba.

Jaridar ta rahoto cewa da zarar Mai martaba Aminu Ado Bayero ya karbi wannan sanda ta girma, zai shiga gidan Sarki da ke cikin fadar Mai martaba a Birnin Kano.

“An kammala shirye-shirye na gabatarwa Mai martaba Sarki sandar girma. Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne zai mika masa sandar.” Inji Majiyar.

Ta ce: “Ko da ya ke gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba ya jihar Kano, amma zai iya dawowa nan ba da dadewa ba, ya mikawa Sarki sandar girma a yau (Talata).”

KU KARANTA: Babban Sakataren Sanusi II ya rubutawa Masarauta wasikar murabus

Ana sa rai yau za a mikawa sabon Sarkin Birnin Kano sandar-girma
Gwamnan Kano zai ba sabon Sarki sandar girma idan ya dawo
Asali: Facebook

Wannan majiya ta yi magana ne da sa ran cewa hakan zai faru a Ranar Talata. Alamu su na nuna cewa har yanzu Gwamna Ganduje bai dawo daga tafiya ba.

Dama can kun ji labari cewa gwamnoni za su yi wata ganawa da shugaban kasa game da rikicin APC. Gwamnan Kano ya na cikin wanda za ayi zama da shi.

Tawagar sabon Sarkin za su yi masa rakiya daga gidansa da ke Mandawari zuwa fada da zarar gwamnatin Kano ta mika masa sandar da ke tabbatar da sarauta.

Bayan gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke Muhammadu Sanusi II, ta nada ‘Dan Marigayi Ado Bayero, kuma Hakimai sun fara yi masa mubaya’a.

s

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng