Ba za a bar tsohon Sarki Sanusi II ya rika ganawa da jama’a ba – Hadimin Ganduje

Ba za a bar tsohon Sarki Sanusi II ya rika ganawa da jama’a ba – Hadimin Ganduje

Sababbin bayanai su na cigaba da fitowa game da yadda rayuwar tsohon Sarkin Birnin Kano, Muhammadu Sanusi II za ta kasance bayan an tsigesa daga kan mulki.

Rahotanni sun zo mana cewa tsohon Mai martaba Muhammadu Sanusi II ba zai samu damar ganawa da Jama’a ba a yayin da ya ke tsare a Kauyen da aka maida shi.

Darekta-Janar na harkokin sadarwa da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana cewa za a cigaba da tsare Muhammadu Sanusi II.

Salihu Tanko Yakassai ya yi karin haske a kan wasu maganganu da ake yi, inda ya ce tsohon Sarkin ba zai samu ko da damar ganawa da Masu kawo masa ziyara ba.

Salihu Yakasai ya yi wannan bayani bayan da wasu su ka fara kira ga tsohon Sarkin na Kano ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 ko ya nemi wata kujerar siyasa.

KU KARANTA: "Da PDP ta fadi zaben 2019 a Sokoto, da an tsige Sarkin Musulmi"

Hadimin na gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ba haka dokar tunbuke Sarki ta ke aiki ba. Hadimin ya ce Sanusi II ba zai samu damar da ake masa hari ba.

Da ya ke jawabi a shafinsa na Tuwita, ya ce: “Babu shakka wasu sun jahilci yadda sauke Sarki ya ke aiki. Idan aka tunbuke Sarki, za a jefa shi wani kungurmin lungu ne.”

“Zai kuma kasance a tsare ne kawai a cikin gidansa. Ba zai samu damar ganin wasu Baki ba. Wanda ke cikin irin wannan hali, ‘yanci zai nema ba zabe mai zuwa ba.”

Yakassai shi ne ya fitar da sanarwar tsige Sarki Sanusi II a Ranar Litinin. Kawo yanzu dai jama’a daga wurare da-dama sun fara ba tsohon Sarkin shawarar ya shiga siyasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel