Sanusi: Tsige ka da aka yi bai dace ba, kuma abin takaici ne inji Obasanjo

Sanusi: Tsige ka da aka yi bai dace ba, kuma abin takaici ne inji Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya rubuta wasika ga tsohon Sarkin Birnin Kano, Muhammadu Sanusi II wanda aka tunbuke daga gadon sarauta.

Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya ya bayyana wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka jiya a matsayin abin takaici kuma wanda sam bai dace ba.

A wannan wasika mai sakin layi uku da ta ke yawo a kafafen yada labarai, tsohon shugaban Najeriyar ya yi wa Sanusi addu’ar yin hakuri da wannan kaddara.

Ya ce: “Na wayi gari yau da safe bayan atisaye ne da ibada da kuma taron safiya da ma’aikatana, sai na samu mummuna kuma kyakkyawan labari na tsige ka.”

“Tsige ka da majalisar zartawar jihar Kano ta yi abin takaici ne domin bai dace ba. Abin farin ciki ne domin ka biya farashin ka.” Obasanjo ya kuma yi masa addu’a.

KU KARANTA: Sanusi II ya koma kauyen Loko da zama bayan an tsige sa

Sanusi: Tsige ka da aka yi bai dace ba, kuma abin takaici ne inji Obasanjo

Obasanjo ya yi wa Sarki Sanusi addu'a bayan tsige sa jiya
Source: Twitter

“Addu’ata ita ce Ubangiji ya ba ka karfin jurewa wannan kaddara, da kuma dacewa a kan janyar da ka dauka domin cigaban al’umma da kuma kasarmu.” Inji sa.

A karshen takardar, Olusegun Obasanjo wanda ya mulki Najeriya a lokacin mulkin Soji da kuma farar hula, ya nuna jinjinarsa ga tsohon Mai martaba Sarki Sanusi II.

Obasanjo ya rubuta wannan wasika ne a Ranar Litinin, 9 ga Watan Maris, 2020. Sai dai babu tabbacin ko wasikar ta isa ga Sanusi II wanda aka tsige a ranar Litinin.

Kawo yanzu dai shugaban kasa mai-ci Muhammadu Buhari bai yi magana game da wannan lamari ba. Bai kuma taya sababbin Sarakunan da aka nada murna ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel